Jikokin Sani Abacha sun fita yawon Shakatawa
Wayasan yanda kyawon jikokintsohon shugaban kasa na soji na Najeriya Sani Abacha yake?
Lokacin bazarane, zaka iya jin dadi son ranka, Sagesse Gumsu yar Sani Abacha da kyawawan yayanta suna jin dadin rayuwarsu a Atlantis, Dubai.
An dauki hoton yaran da kyakyawar uwarsu ba da dadewa ba suna wasa da Dolphin, a gurin da aka tana da don ajiye Dolphin a Dubai.
Iyalin Sani Abacha suna cikin sanannun iyali a kasar Najeriya, maganar gaskiya, tarihin kasar Najeriya baya kammaluwa in ba'a ambaci sunan Abacha ba.
Sani Abacha sojin Najeriya ne kuma dan siyasa, wanda ya mulki Najeriya daga shekara ta 1993 zuwa 1998. Lokacin mulkin Abacha yazo da ruda ni, duk da cewa an samu habakar arziki, kuma anci mutum cin hakkin dan adam.
Asali: Legit.ng