Kasafin kudin 2022 ya wuce karatu na biyu a majalisar wakilai
- Majalisar wakilai ta zartar da kasafin kudin 2022 kwanaki bayan gabatarwar shugaban kasa Buhari
- A bayan majalisar dattawan Najeriya ta zartar da kasafin duk dai mako guda bayan gabatar da kasafin a gayammar majalisar dokoki
- Gaba da majalisun sun tafka muhawara kafin daga baya ta wuce zama na biyu a zaman majalisu
Abuja - Daily Trust ta rahoto cewa, majalisar wakilai a ranar Alhamis 14 ga watan Oktoba ta zartar da kasafin kudin 2022 na naira tiriliyan 16.39 don wuce karatu na biyu na majalisa.
Wannan ya biyo bayan kammala muhawara kan manyan ka'idojin kasafin na shekarar 2022.
Majalisar dattijai, a ranar Laraba , ta zartar da Dokar Kasafin Kudi ta 2022 a karatu na biyu bayan sama da awa daya ana muhawara kan manyan ka'idojin ta.
Daidai da mako guda da ya gabata kenan da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kudirin kasafin kudin na Naira tiriliyan 16.39 na kasafin kudin shekarar 2022 ga gamayyar majalisar dokokin Najeriya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kasafin kudin 2022 da Buhari ya ba majalisa ya tsallake caccaka a zama na biyu
Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, takardun kasafin kudi na 2022 sun wuce karatu na biyu a majalisar dattawa.
Majalisar dattawan ta zartar da kasafin kudin ranar Laraba 13 ga watan Oktoba bayan muhawara kan manyan ka'idojin ta na tsawon kwanaki biyu.
Da yake ba da gudummawa ga muhawarar, Enyinnaya Abaribe, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta dakile abin da ya bayyana a matsayin "cin bashi".
Shugaban marasa rinjaye ya ce ya kamata Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tsaya kan aikinsa na sarrafa tattalin arzikin kasar.
Wani Gwamna Ya Umurci Dalibai Da Ma’aikatan Gwamnatin Jiharsa Su Fara Sanya Kayan Gargajiya Ranar Juma’a
Wasu sanatoci da dama sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara gudanar da ayyukan gine-gine a fadin kasar nan.
Da yake jawabi a karshen muhawara kan kasafin kudin, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ce rance ba laifi bane muddin ana amfani da shi ga abin da aka ware don shi.
Shugaban majalisar dattawa ya ce ya kamata majalisar kasa ta iya kammala zartar da kasafin kafin watan Disamba.
A makon da ya gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi na naira tiriliyan 16.39 ga wani zaman gamayyar majalisar dokokin kasar.
A cikin kasafin, gwamnatin Buhari ta ware makudan kudaden da suka kai Naira miliyan 650 don fara aikin wutar Mambila, kudin da ya yi kasa da biliyan daya, inji rahoton Daily Trust.
Gwamna El-Rufai ya gabatar da kasafin kudin 2022 ga majalisar dokokin Kaduna
A wani labarin, Gwamna Malam Nasiru El-Rufai ya gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2022 na naira biliyan 233 ga majalisar dokokin jihar Kaduna a yau Talata 12 ga watan Oktoba.
Kasafin kudin yana dauke da bayanin kashe Naira biliyan 146 a fannin ayyuka da jari da kuma na Kashewa akai-akai da suka kai Naira biliyan 87.6 a shekarar.
El-Rufa'i ya yi nuni da cewa rabe-raben da aka yi a cikin alkaluman kasafin kudin na shekarar 2022 sun yi nuni da kimar siyasa da ka'idojin shugabanci wanda a koda yaushe suke jagorantar kasafin kudi shida na baya da gwamnatinsa ta gabatar.
Asali: Legit.ng