Ana kishin-kishin wani gagarumin sauya sheka yayin da shugaban APC ya gana da shahararren gwamnan PDP

Ana kishin-kishin wani gagarumin sauya sheka yayin da shugaban APC ya gana da shahararren gwamnan PDP

  • Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC mai mulki, Mai Mala Buni, ya haddasa sabbin rade-radi na sauya sheka
  • Hakan ya kasance ne bayan gwamnan jihar Yobe ya ziyarci takwaransa na Adamawa, Ahmadu Fintiri, wanda yake jigo ne a jam’iyyar PDP
  • Tun bayan da Buni ya karbi ragamar shugabancin APC, gwamnonin PDP uku ne suka koma jam’iyyar mai mulki

Yola, jihar Adamawa - Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Mai Mala Buni, a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, ya gana da gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri.

Buni wanda ya kuma kasance gwamnan jihar Yobe ya yada hotunan ganawarsa da Fintiri a shafin Facebook, yana mai godiya ga takwaran nasa na Adamawa bisa irin tarbar da yayi masa.

Kara karanta wannan

Shugabancin kasa a 2023: Tinubu na kara samun goyon baya, ya gana da tsohon shugaban majalisar dattawa

Ana kishin-kishin wani gagarumin sauya sheka yayin da APC ya gana da shahararren gwamnan PDP
Ana kishin-kishin wani gagarumin sauya sheka yayin da APC ya gana da shahararren gwamnan PDP Hoto: Hon Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Ya rubuta a shafin nasa cewa:

"Muna godiya ga Maigirma Gwamnan Jihar Adamawa Mai Girma Alhaji Ahmadu Fintiri da mutanen jihar masu karamci kan kyakkyawar tarbar da suka yi mana."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ganawar ya haifar da rade-radin sauya sheka

Tun bayan da Gwamna Buni ya karbi ragamar shugabancin jam’iyyar APC, gwamnonin PDP uku da suka hada da, David Umahi na Ebonyi, Ben Ayade na Cross River, da Bello Matawalle na Zamfara ne suka koma jam’iyyar mai mulki daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Saboda haka, ziyarar da ya kai Adamawa ya haifar da sabbin rade-radin cewa watakila wani sauya sheka na nan zuwa nan kusa kasancewar gwamna Fintiri dan PDP ne.

Da yake martani a Facebook, Sabiu Abdu Azare ya ce:

"Kuna so kasar nan ta dunga gudanar da tsarin jam'iyya daya."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: APGA ta yi martani, ta bayyana dalilin da yasa mataimakin gwamnan Anambra ya sauya sheka zuwa APC

Usman Aliyu ya ce:

"Ka ci gaba da babban aiki yallabai, yayin da kake ci gaba da kasancewa dan dimokradiyya na gaskiya tare da gagarumin gogewa game da abin da ya kamata siyasa ta kasance da abin da ake bukata don aiwatar da aikin gaba daya ...
"Lallai, muna addu'a da fatan ɗan'uwanka daga Adamawa zai kasance a jam’iyyar All Progress Congress yayin da kake ci gaba da yi musu wa'azin gina babban jirgi fiye da ba mutane damar ci gaba da tafiya cikin karamin jirgin ruwa ..."

Mustapha Hadejia yace:

"Gwamnan jihar Adamawa kofar a bude take barka da zuwa Apc."

Mataimakin gwamnan jihar Anambra ya sauya sheka zuwa APC, ya gana da Buhari

A gefe guda, mun kawo a baya cewa mataimakin gwamnan jihar Anambra, Nkem Okeke, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, ya karbi bakuncin Shugaban kwamitin riko na APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, mataimakin gwamnan Anambra, Dr. Nkem Okeke da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasan Arewa 10 da ke kan gaba wajen neman kujerar shugaban Jam’iyyar PDP

Mataimakin shugaban kasa a shafukan sadarwa ta zamani, Buhari Sallau ne ya bayyana labarin sauya shekar tasa a wata sanarwa a Facebook.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng