Yanzu Yanzu: APGA ta yi martani, ta bayyana dalilin da yasa mataimakin gwamnan Anambra ya sauya sheka zuwa APC
- Jam'iyyar APGA ta yi martani a kan sauya shekar mataimakin gwamnan Anambra zuwa jam'iyyar APC mai mulki
- Sakataren jam’iyyar APGA na kasa, Tex Okechukwu, ya ce sauya shekar nasa bai zo masu a bazata ba domin abu ne da suke ta tsammani
- Sai dai kuma ya ce hakan ba zai girgiza jam’iyyar ba gabannin zaben gwamna na ranar 6 ga watan Nuwamba
Abuja - Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta yi martani a kan sauya shekar mataimakin Gwamnan jihar Anambra, Dr Nkem Okeke, zuma jam’iyyar All Progressives Congress.
A wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, sakataren jam’iyyar APGA na kasa, Tex Okechukwu, ya ce matakin mataimakin gwamnan ba zai girgiza jam’iyyar ba gabannin zaben gwamna na ranar 6 ga watan Nuwamba.
Ya kara da cewa sauya shekar abu ne da aka dade ana tsammani tun da Okeke na ta gaba da kowa kan rashin samun tikitin takarar gwamana na jam’iyyar, Channels TV ta ruwaito.
Ya ce:
“Mataimakin gwamnan ya yi zaton cewa gwamna Willie Obiano da jam’iyyar za su bashi tikitin takarar Gwamnan jam’iyyar a zaben fidda gwani da aka yi a bagas.
“Da hakan bai faru ba, sai ya fara nuna wasu bakin halaye da kauracewa ayyuka.”
Sai dai Okechukwu ya bayyana cewa APGA na kallon ficewar mataimakin gwamnan ba tare da sanarwa ba zuwa ga hukumar ko ubangidansa a hukumance ba daidai bane domin gwamnan na mutunta shi da kauna.
A cewarsa, jam'iyyar ta yi Allah wadai da yadda jam'iyyar adawa ta APC ke nuna maitarta a fili yayin shirye-shiryen zaben gwamna, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Kakakin na APGA ya yi kira ga dukkan mambobin jam’iyyar da su ci gaba da hada kansu don tabbatar da sun lashe zabe da tazara mai yawa.
Mataimakin gwamnan jihar Anambra ya sauya sheka zuwa APC, ya gana da Buhari
A baya mun kawo cewa, mataimakin gwamnan jihar Anambra, Nkem Okeke, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, ya karbi bakuncin Shugaban kwamitin riko na APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, mataimakin gwamnan Anambra, Dr. Nkem Okeke da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.
Mataimakin shugaban kasa a shafukan sadarwa ta zamani, Buhari Sallau ne ya bayyana labarin sauya shekar tasa a wata sanarwa a Facebook.
Asali: Legit.ng