Da dumi-dumi: Mataimakin gwamnan jihar Anambra ya sauya sheka zuwa APC, ya gana da Buhari

Da dumi-dumi: Mataimakin gwamnan jihar Anambra ya sauya sheka zuwa APC, ya gana da Buhari

  • Mataimakin gwamnan jihar Anambra, Dr Nkem Okeke ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress
  • Okeke ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba
  • Shugaban APC, Mai Mala Buni da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ne suka yi masa rakiya zuwa Villa

Mataimakin gwamnan jihar Anambra, Nkem Okeke, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, ya karbi bakuncin Shugaban kwamitin riko na APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, mataimakin gwamnan Anambra, Dr. Nkem Okeke da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.

Da dumi-dumi: Mataimakin gwamnan jihar Anambra ya sauya sheka zuwa APC, ya gana da Buhari
Da dumi-dumi: Mataimakin gwamnan jihar Anambra ya sauya sheka zuwa APC, ya gana da Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban kasa a shafukan sadarwa ta zamani, Buhari Sallau ne ya bayyana labarin sauya shekar tasa a wata sanarwa a Facebook.

Kara karanta wannan

Kano da sauran jihohi 7 da aka samu rabuwar kai a APC, aka zabi shugabanni 2 a jiha

Ya rubuta a shafin nasa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tarbi shugaban kwamitin rikon kwarya na APC na kasa yayin da mataimakin gwamnan Anambra ya koma APC a fadar shugaban kasa a ranar 13 ga watan Oktoba 2021.
“Shugaba Buhari tare da shugaban kwamitin riko na APC kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, mataimakin gwamnan Anambra Dr. Nkem Okeke da gwamnan Imo Hope Udodinma yayin da mataimakin gwamnan Anambra ya koma APC a fadar gwamnati a ranar 13 ga Oktoba 2021.”

Shugaba Buhari ya shiga labule da Gwamna Obaseki a fadar shugaban kasa

A wani labarin, mun kawo a baya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, a fadar shugaban kasa da ke babbar birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Jerin Jiga-jigan APC 10 da suka kai karar Gwamna Ganduje wajen uwar Jam’iyya

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin labarai, Mista Femi Adesina ne ya bayyana hakan yayin da ya wallafa hotunan ganawar tasu a shafinsa na Facebook.

Sai dai bai bayar da cikakke bayani kan abun da ganawar tasu ta kunsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng