Wani mutum ya datse 'yar yatsar jami'in ɗan sanda da cizo a Legas

Wani mutum ya datse 'yar yatsar jami'in ɗan sanda da cizo a Legas

  • Yan sanda sun gurfanar da wani Samuel Jacob da ake zargi da cizon yatsar jami'in dan sanda
  • Rundunar 'yan sandan ta bakin mai shigar da kara ta yi zargin Jacob ya antayawa dan sanda man fetur
  • Sai dai wanda ake tuhuma da aikata laifukan ya musanta kuma alkalin kotu ya bada belinsa kan N200,000

Legas - An gurfanar da wani mutum mai shekaru 29, Samuel Jacob, a gaban alkalin kotun Majistare da ke Badagry a Legas, a ranar Talata, kan tuhumarsa da cije 'dan yatsar dan sanda, Saja Musa Hassan.

'Yan sandan na tuhumar Jacob, wanda ba a bayyana adireshinsa ba da laifin duka da yin rauni kamar yadda ta zo a ruwayar The Punch.

Wani mutum ya datse 'yar yatsar jami'in ɗan sanda da cizo a Legas
Gudumar alkalin kotu. Hoto: Daily Trust
Source: UGC

Read also

An yanke wa Salisu ɗaurin gidan yari kan satar tukwane da kujeru a coci a Legas

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Clement Okuiomose ya shaidawa kotu cewa wanda aka yi kararsa ya aikata laifin ne a ranar 3 ga watan Oktoba misalin karfe 11.30 na safe a Oloko, Badagry a Legas.

Okuiomose, ya kuma ce wanda ake kararsa ya antayawa Saja Hassan fetur a yayin da ya ke gudanar da aikinsa da doka ta halasta masa, ruwayar The Punch.

Laifin, a cewar da sanda mai shigar da karar ta saba wa sashi na 246 da 174 da dokar masu laifi na jihar Legas na shekarar 2015.

Abin da wanda ake zargi yace?

Amma wanda aka gurfanar ya musanta aikata laifukan da ake zarginsa.

Alkalin kotun, Mr Fadaunsi Adefioye, ya bada belin wanda ake zargin a kan kudi Naira Dubu Dari Biyu (N200,000) da kuma mutane biyu wadanda za su tsaya masa.

Abin da yasa Legas ta zama matattaran mashaya, muggan ƙwayoyi, Kakakin Majalisa Obasa

Read also

Magidanci ya kashe matarsa saboda ta raina bajintarsa wurin kwanciyar aure

A wani labarin, kakakin majalisar jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya yi alkawarin cewa majalisar jihar za ta cigaba da goyon bayan yakin da ake yi da shan miyagun kwayoyi a jihar da illar da hakan ke yi wa matasa da mazauna jihar.

A ruwayar The Punch, Obasa ya yi wannan alkawarin ne yayin da ya karbi bakuncin jami'an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, da kwamandan jihar, Ralph Igwenagu ya yi wa jagoranci.

Kakakin majalisar ya ce yana fatan idan aka hada hannu wurin yaki da matsalar hakan zai taimaka wurin inganta lafiyar mutanen Legas.

Source: Legit.ng

Online view pixel