Mu Buhari bai taba ganin mu ba – Jigon APC ya yi Allah-wadai da karbar Fani-Kayode a Aso Villa

Mu Buhari bai taba ganin mu ba – Jigon APC ya yi Allah-wadai da karbar Fani-Kayode a Aso Villa

  • Reno Omokri yace Femi Fani-Kayode ya ci amanar Igboho da Nnmadi Kanu
  • Shi ma Joe Igbokwe ya yi tir da yadda aka karbi Cif Fani-Kayode a Aso Villa
  • Jigon na APC yace gwamnatin su ba ta taimakon na gida, sai makiyan waje

Abuja - Reno Omokri wanda ya yi aiki a fadar shugaban kasa lokacin Goodluck Jonathan, ya zargi Femi Fani-Kayode da yaudarar abokan gwagwarmayarsa.

Punch ta rahoto Reno Omokri yana cewa tsohon Ministan ya ci amanar shugabannin fafutukar kasar Yarbawa da Biyafara Sunday Adeyemo da Nnamdi Kanu.

Omokri ya bayyana wannan ne a kafofin sadarwa na zamani a ranar Juma’a, 17 ga watan Satumba, 2021, yana tir da sauya-shekar da jigon adawan kasar.

Hadimin tsohon shugaban kasar yana mamakin yadda tsohon Ministan zai dawo APC ya yi ta zargin gwamnatin tarayya da kassara Kanu da Sunday Ighoho.

Kara karanta wannan

Karya Fani-Kayode ya sharara, babu hannunsa a sauya-sheka ta daga PDP inji Gwamnan APC

FFK ya yaudari Igboho da shugaban IPOB

Jaridar tace Omokri ya kamanta Fani-Kayode da ‘Judas Iscariot’, wanda ya yaudari Yesu, duba da watsi da ‘yanuwan na sa da ke tsakar gwagwarmaya da ya yi.

Da yake bayani, Omokri yace shigo war tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani cikin jam’iyyar PDP, ya fi masu amfani kan rasa Fani-Kayode zuwa APC.

Fani-Kayode
Fani Kayode da Matawalle Hoto: hausa.premiumtimesng.com
Asali: UGC

“PDP ta rasa FFK ta tashi da @ShehuSani. Kamar in ce Manchester United ta rasa Sergio Romero ne, amma ta samu Cristiano Ronaldo. An taki sa’a!”

Joe Igbokwe ya fito yana babatu

Shi kuma jigon APC a Legas, Joe Igbokwe, ya soki sauya-shekar Fani-Kayode da yadda shugaba Muhammadu Buhari ya yi masa kyakkyawar tarba a Aso Villa.

Da yake magana a Facebook, Igbokwe ya koka, yace shugaban kasa bai taba gayyatar wadanda suka yi shekaru a APC ba, sai aka hangi Fani-Kayode a gefensa.

Kara karanta wannan

Mayaudarin dan Oduduwa: Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki Fani Kayode bayan komawa APC

“Duk kokari na a APC, ba a taba kira ta a waya daga Abuja ba, ko a kira ni in sha shayi. Amma sai ga shi an shimfida wa karuwan siyasa dadduma a Abuja.”
“APC na yi wa makiya alheri, ta shagwaba su. Wannan rayuwa dai to. Daruruwa sun bauta wa APC amma babu ko katin waya, babu kwalban lemu ko nagode.”

Umahi ya dura kan FFK

Dazu aka ji Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi yana caccakar Femi Fani Kayode, yace karya yake yi, babu hannunsa a sauya-shekarsa zuwa jam’iyyar APC.

Gwamnan na Ebonyi yayi wa Fani-Kayode kaca-kaca, yace ya janye kalaman da ya yi a jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel