Minista ya sanar da kotu yadda Zainab Yar'adua ta yi takardun bogi don mallakar fili a Abuja

Minista ya sanar da kotu yadda Zainab Yar'adua ta yi takardun bogi don mallakar fili a Abuja

  • Ministan FCT, Muhammad Bello, a ranar Talata ya sanar da babbar kotun tarayya yadda Zainab Yar'Adua ta mallaki fili a Abuja da takardun bogi
  • Zainab ta maka mutum hudu gaban wata babbar kotun tarayya a Abuja kan cewa za su cinye mata wani fuloti nata da ke gundumar Kado
  • Sai dai ministan ya ce tun kafin nan, Zainab ta bada bayanai 2 mabanbanta kan mallakar filin, ta ce ta siya ne, daga baya ta ce an ba ta ne

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya, Malam Muhammad Musa Bello a ranar Talata ya sanar da wata babbar kotun Abuja cewa diyar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'Adua, Zainab, ta samu wasu takardun bogi domin mallakar wani fuloti da ake rigima kan shi a Abuja.

Ministan ya jaddada cewa babu wata shaida da ke nuna cewa diyar tsohon shugaban kasan ta taba neman mallakar filin a hukumance ko kuma ta taba biyan kudi domin ta mallaki filin, PRNigeria ta ruwaito.

Read also

Kotun daukaka kara ta sa ranar yanke hukunci kan bukatar sauke Buhari da nada Atiku

Minista ya sanar da kotu yadda Zainab Yar'adua ta yi takardun bogi don mallakar fili a Abuja
Minista ya sanar da kotu yadda Zainab Yar'adua ta yi takardun bogi don mallakar fili a Abuja. Hoto daga PRNigeria.com
Source: UGC

A wata takardar hadin guiwa da masu kare kansu suka fitar kan musanta mallakar fuloti mai lamba 506, Zone B 09, gundumar Kado a Abuja, ministan da hukumar habaka babban birnin tarayyan sun musanta taba bada filin ga diyar tsohon shugaban kasan.

A takardar mai kwanan wata 21 ga watan Satumba kuma aka shigar a madadin lauyansu, Yakubu Abubakar, ministan da hukumar FCDA sun sanar da kotun cewa Zainab na ikirarin filin na ta ne ta hanyar amfani da karfin ikon antoni janar na wancan lokacin.

Zainab ta hannun kamfanin ta mai suna Marumza Estate Development Company Limited ya maka Itban Global Resources Limited, Haliru Malami, ministan FCT da FCDA gaban wata kotun tarayya da ke Abuja inda ta ke ikirarin mallakar fuloti mai lamba 506, Zone B 09, gundumar Kado da ke Abuja wanda ta ce ta siya daga FCDA ta hannun Itban Global Resources da Malami.

Read also

Hotunan Osinbajo na gudu a filin motsa jiki yayin karbar bakuncin gasar Baton

Amma kuma a wata takarda, masu kare kansu na uku da na hudu sun ce kafin Zainab ta shigar da karar, ta bada bayanai mabanbanta kan yadda ta samu filin ta hannun wani tsohon ministan FCT kuma ta ce ta siya daga hannun Haliru Malami.

Femi Adesina: FG na samun cigaba a fannin yakar rashin tsaro, jama'a ne ba su gani

A wani labari na daban, mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce gwamnatin tarayya ta na cigaba da samun nasarori kan yaki da rashin tsaro a kasar nan.

Har a yanzu, ana cigaba da samun matsalolin garkuwa da mutane, 'yan fashin daji da kuma harin da 'yan bindiga ke kaiwa a fadin kasar nan, TheCable ta ruwaito.

A yayin jawabi a ranar Litinin yayin tattaunawa da gidan Talabijin na Channels, Adesina ya ce duk wanda ke duba kokarin gwamnatin nan ba zai hada shi da na gwamnatin da ta gabata ba.

Read also

Gwamnatin Dubai ta gwangwaje Jaruma Saratu Daso da kyautar dalleliyar sabuwar mota

Source: Legit.ng

Online view pixel