Gwamnatin Dubai ta gwangwaje Jaruma Saratu Daso da kyautar dalleliyar sabuwar mota

Gwamnatin Dubai ta gwangwaje Jaruma Saratu Daso da kyautar dalleliyar sabuwar mota

  • A safiyar Alhamis ne jarumar Kannywood, Saratu Daso ta bayyana cewa gwamnatin Dubai ta ba ta kyautar mota
  • A wasu hotuna da jarumar ta wallafa a shafin ta na Instagram, an gan ta da wata leda rike tare da hoton motar
  • Tuni masoyan jarumar tare da abokan aikin ta suka fara tururuwar yi mata fatan alkhairi kan wannan kyautar

Gwamnatin Dubai ta gwangwaje jarumar Kannywood, Saratu Gidado, wacce aka fi sani da Daso da sabuwar dalleliyar mota.

Kamar yadda jarumar ta wallafa a shafin ta na Instagram a safiyar Alhamis, ta sanar da cewa gwamnatin Dubai ta ba ta kyautar sabuwar mota fil.

Gwamnatin Dubai ta gwangwaje Jaruma Saratu Daso da kyautar dalleliyar sabuwar mota
Gwamnatin Dubai ta gwangwaje Jaruma Saratu Daso da kyautar dalleliyar sabuwar mota. Hoto daga @saratudaso
Asali: Instagram

Kara karanta wannan

Magidanci ya kashe matarsa saboda ta raina bajintarsa wurin kwanciyar aure

Tuni masoyan jarumar, 'yan uwa da abokan aikin ta suka dinga tururuwa tare da taya ta murna da kuma fatan alkhairi.

Tashar Africa Magic ta DSTV na shirin wasan kwaikwayo kan uwargidar Buhari

A wani labari na daban, Africa Magic, gagarumin kamfanin nishadantarwa mallakin MultiChoice, su na duba yuwuwar yin wasan kwaikwayo kan Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Busola Tejumola, shugaban tashar ta Najeriya, ta bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ta ke jawabi a taron kwana biyu da Africa Magic ta shirya na baje koli a jihar Kano, wanda aka kammala jiya.

A takardar da MultiChoice ta fitar, taron da ta shirya an samu ya hade da taron shekara- shekara na kungiyar watsa labarai na Najeriya, BON, ya samar da dama ga furodusoshi wurin mu'amala kai tsaye da Africa Magic domin samun damar tallatawa da siyar da hajojinsu.

Kara karanta wannan

Hotunan Osinbajo na gudu a filin motsa jiki yayin karbar bakuncin gasar Baton

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng