Miyagun yan bindiga sun bude wa masallata wuta, Sun kashe aƙalla 10 a jihar Katsina
- Wasu yan bindiga sun sake kai hari ƙaramar hukumar Batsari, dake cikin jihar Katdina domin ɗaukar fansa
- Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wa mutanen dake sallar magariba wuta a ƙauyen Yasore
- Kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Gambo Isa, yace aƙalla mutum 10 sun mutu, wasu 11 sun jikkata
Katsina - Rahotanni sun nuna cewa aƙalla masallata 10 aka kashe yayin da wasu miyagun yan bindiga suka shiga ƙauyen Yasore, ƙaramar hukumar Batsari, jihar Katsina.
Dailytrust ta rahoto cewa lamarin ya auku ne lokacin da mutanen ke tsaka da sallar Magrib ba zato yan bindigan suka buɗe musu wuta, ranar Talata.
Legit.ng Hausa ta gano cewa tuni aka gudanar da jana'izar waɗanda suka rasu da safiyar ranar Laraba, yayin da waɗanda suka ji raunuka aka kaisu asibiti.
Daga ina maharan suka fito?
Rahoto ya bayyana cewa maharan sun fito ne daga wata maɓoyarsu a dajin birnin Gwari dake jihar Kaduna.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yan bindigan, waɗanda suka farmaki ƙauyen da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, sun kuma kona gidaje da dama a garin.
Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa maharan sun shigo ƙauyen duk da kokarin da sojoji da yan sanda ke yi.
Mutumin yace:
"Mun ga irin nasarorin da sojoji suka samu kan yan ta'adda a yan kwanakin nan saboda harin su yayi sauki sosai ba kamar a baya ba, amma har yanzun manoma na tsoron girbo abinda suka noma."
Ya ƙara da cewa mafi yawan mazauna ƙauyen, waɗanda suka tsira daga mummunan harin sun tsere zuwa hedkwatar ƙaramar hukumar Batsari.
Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?
Da yake tabbatar da harin, kakakin rundunar yan sanda reshen jihar, SP Gambo Isah, yace maharan sun kai wannan harin ne domin ɗaukar fansa kan yan Bijilanti.
"Yan bindigan sun.kai harin ɗaukar fansa ne. Mutum 10 sun mutu yayin da wasu 11 kuma suka jikkata."
A wani labarin kuma Kalli Hotunan yadda miyagun yan bindiga suka kai wani mummunan hari a jihar Zamfara
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kashe mutane da dama tare da ƙona gidaje da motoci.
Wannan hari na zuwa ne bayan gwamnati ta ɗauki tsauraran matakai cikinsu harda katse sabis a jihar.
Asali: Legit.ng