Kannywood: Auwal West ya yi sabon bidiyo yana mai ba Hadiza Gabon hakuri

Kannywood: Auwal West ya yi sabon bidiyo yana mai ba Hadiza Gabon hakuri

  • Jarumin Kannywood Auwal Isah West ya fito ya bai wa abokiyar sana’arsa, Hadiza Gabon hakuri kan raddi da yayi mata
  • Auwal dai ya caccaki Gabon ne kan shagube da tayi wa wasu manyan jaruman masana'antar da suka yi hotuna da gwarzon cin gasar BBNaija
  • Ya ce duk abubuwan da ya fadi a baya kan Gabon ya fade su ne bisa bacin rai da zafin zuciya

Shahararren jarumin Kannywood, Auwal Isah West ya fito ya bai wa abokiyar sana’arsa, Hadiza Gabon hakuri kan raddin da yayi mata sakamakon caccakar wasu manyan jaruman masana’antar da tayi.

Hadiza dai tayi wani rubutu a shafinta na Instagram inda tayi shagube ga wasu manyan jarumai da daraktocin masana’antar da suka halarci wani liyafa da kamfanin Multichoice ta shiryawa wadanda suka lashe gasar BBNaija.

Read also

Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari

Kannywood: Auwal West ya yi sabon bidiyo yana mai ba Hadiza Gabon hakuri
Kannywood: Auwal West ya yi sabon bidiyo yana mai ba Hadiza Gabon hakuri Hoto: Naijaloaded.com
Source: UGC

Hotunan jarumai irin su Ali Nuhu, Rashida mai Sa’a, Naziru dan Hajiya, Bashir Mai shadda, Adam Zango, da dai sauransu yayi ta yawo a kafafen sadarwa tare da gwarzon BBNaija, White Money.

Sai dai a wallafar da tayi a shafin nata, Gabon ta zarge su da shishigi inda tace ko saka hotunan gwarzon gasar bai yi ba a shafinsa.

Wannan ya arzuka Auwal West inda har yayi mata sharhi da cewa wadannan mutane da take Magana a kai sune suka daukaka ta har duniya ta santa.

Sai dai kuma a wani bidiyo da shafin gaskiyazalla ya wallafa a Instagram, An gano Auwal West yana bai wa jarumar, iyaye da masoyanta hakuri a kan furucin da yayi a baya, yana mai cewa bacin rai ne yasa ya fadi abun da ya fada.

Read also

Duk da komawa APC, da alamu Fani-Kayode zai fuskanci fushin kotu saboda badakala

Ya ce:

“Salamu alaikum, sunana Auwal West. Duk abubuwan da na fada a kan Hadiza Gabon ba kamar kalma da na fada na zancen kawalinta, ni ban san wannan maganar ba bacin rai shi ya kawo haka, amma ina mai ba iyayenta hakuri da yan uwanta da masoyanta, nayi ba daidai ba nayi mata kuskure halin zuciya ce amma dan Allah dan Annabi tayi hakuri, nagode.”

Ga bidiyon a kasa:

Bidiyon Auwal West yana caccakar Hadiza Gabon kan hannunka mai sanda da tayi wa wasu manyan Kannywood

A baya mun kawo cewa Auwal Isah West ya caccaki abokiyar sana’arsa, Hadiza Gabon bayan tayi hannunka mai sanda ga wasunsu da suka halarci taro da kamfanin multichoice ta shirya.

Kamfanin dai ya shirya taron liytafar ne na karrama ‘wadanda suka lashe gasar BBNaija a garin Kano, inda manyan jarumai irin su Ali Nuhu, Rasheeda mai Sa’a, darakta Bashir Mai Shadda, Naziru Danhajiya da sauransu suka halarta.

Read also

Bidiyon Auwal West yana caccakar Hadiza Gabon kan hannunka mai sanda da tayi wa wasu manyan Kannywood

Sai dai kuma, Jaruma Hadiza Gabon ta caccaki abokan sana'arta da yiwa whitemoney wanda ya lashe gasar shishigi. Sannan tace duk rawar jikin da suka dunga yi bai daura su a shafinsa na sosjhiyal midiya ba.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel