MURIC ta goyi bayan malamai suke ladabtar da dalibai a makarantun Islamiyya

MURIC ta goyi bayan malamai suke ladabtar da dalibai a makarantun Islamiyya

  • Kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC ta bayyana matsayar ta kan dukan wasu dalibai a jihar Kwara
  • Kungiyar ta ce, ya kamata gwamnatin jihar ta sake duba lamarin tare da yin bincike mai zurfi a kai
  • Hakazalika, kungiyar ta bayyana cewa, ya kamata iyaye su zama tsayayyu kan 'ya'yansu kuma su daina sakewa

Lagos - Shahararriyar kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC ta yi martani kan abin da ya faru da ta kira mara dadi na cin zarafin dalibai a wata makarantar Islamiyya a jihar Kwara.

MURIC ta nemi gwamnatin jihar da ta duba bidiyon da ake yadawa cikin tsanaki tare da bincikar lamarin yadda ya dace.

Kungiyar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin 11 ga watan Oktoba, wacce Legit.ng Hausa ta samo dauke da sa hannun shugaban na MURIC, Farfesa Ishaq Akintola.

Kara karanta wannan

An dakatar shugaban wata makarantar Larabci da aka ci zarafin wata daliba

Najeriya ba Landan ba: MURIC ta yi martani kan hukunta dalibar Islamiyya a Kwara
MURIC ta yi martani ga gwamnatin Kwara | Hoto: Farfesa Is-Haq Akintola, gwamnatin jihar
Asali: Facebook

Kungiyar ta yi kira ga iyaye da su sanya ido kan 'ya'yansu, tare da tarbiyyantar dasu kamar yadda addinin Islama ya tanada.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da take Allah wadai kan hukuncin cin zarafi da makarantar ta bayar a yi kan wasu dalibai ta hanyar bulala tare da bayyana matsayar ta kan hukunta hukumar makarantar, MURIC ya bayyana cewa:

"Duk da cewa muna daukar hukuncin da aka yanke wa daliban a matsayin mai tsauri, amma muna kula da cewa bai kamata a zartar da hukuncin hukumomin makarantar a kebe ba. Ba zai yiwu a yi watsi da gaskiyar cewa iyaye sun nemi makarantar ta ladabtar da yaransu ba."

MURIC ta ce, an kuma gano wani bidiyon da ke nuna daliban inda suke amsa cewa, sun aikata munanan laifuka ciki har da shan giya da wanka da ita, a cewar MURIC, wannan ba tarbiyyar musulunci bane, kuma ba abin yarda bane.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan sa-kai sun kashe Limami da wasu mutane 10 a Sokoto

Ta kara da cewa, makarantun Islamiyya wuraren karantar da tarbiyya da natsuwa ne, kuma abin kunya ne a samu faruwar irin wadannan abubuwa.

Matsalar bacin tarbiyya

Da take bayyana musabbabin matsalolin tarbiyya, MURIC ta ce:

“Tabarbarewar tarbiyya wanda al'ummar Najeriya ta fada cikinsa shine ke haifar da mafi yawan masifun da ke fuskantar mu a kasar nan a yau.
"Yanzu 'yan Najeriya suna sake kan 'ya'yansu. An sheke kima da ka'idojin iyali da aka sani. Iyaye suna barin yaransu su juya su. Maimakon iyaye su yi wa 'ya'yansu fada da hukunta su saboda hakan, yanzu sai dai su yarda kuma su hada kai dasu.
"Wannan ba kamar a baya ba lokacin da uwa za ta galla wa yaro mari mai kyau sai ya girgiza kuma zai fara rokon uwar kada ta fadawa mahaifinsa idan ya dawo gida."

A cewar MURIC, irin wannan hukunci na tarbiyya shi ake samu a makarantun Islamiyya, amma ana kokarin dakile shi a yanzu, kuma hakan kuskure ne.

Kara karanta wannan

Wasanni: Kasar Saudiyya ta saye kungiyar kwallon kafa ta Newcastle

MURIC ta kuma bayyana cewa, nan Najeriya ne, ba kasar Landan ba da yaro kan iya kiran 'yan sanda ga iyayensa saboda sun masa tsawa ba.

Hakazalika ba Amurka ba ne inda sai uwa ta nemi umarni kafin ta wanke masa jiki ko datti, nan Najeriya ce, kuma zuciyar Afrika da aka sani da tarbiyyantar da 'ya'ya.

MURIC ta goyi bayan a hukunta yara, ta ce rashin haka ke sanya wa su shiga BBNaija

A bangare guda, MURIC ta goyi bayan iyaye da malamai masu ladabtar da dalibai kan kura-kuran da suka aikata, tare da bayyana masu yin sake a matsayin masu goyon bayan abin kunya da shashashanci.

“Muna yabawa iyayen yaran da suka umarci hukumomin makarantar da hukunta yaransu. Adalci zai lissafa su a cikin masu bin addini sau da kafa da ladabtarwa a Najeriya.
"Wadanda ke Allah wadai da iyaye da malamai a yau sune wadanda za su yi farin cikin karfafawa 'ya'yansu da danginsu wajen shiga cikin shirin zinace-zinace na abin kunya na BBNaija a bainar jama'a.

Kara karanta wannan

Rushe-rushe: Makaranta ta bayyana abin da ya sa aka rugurguza gidajen mutane 160 a Zaria

An dakatar shugaban wata makarantar Larabci da aka ci zarafin wata daliba

A baya kadan, Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, gwamnatin Kwara ta fara gudanar da bincike kan cin zarafin wata daliba a makarantar Larabci da malamai suka yi.

Gwamnati ta kafa kwamitin bincike, wanda ya kunshi malaman Muslunci, shugabanni da jami’an gwamnati, domin duba lamarin yayin da aka dakatar da shugaban makarantar har sai an kammala bincike.

Sanarwar da Kwamishinan Ilimi da Ci Gaban Bil Adama, Hajiya Sa’adatu Modibbo Kawu ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa gwamnati ta kuma kai daliban da abin ya shafa zuwa asibitin gwamnati don duba lafiyarsu da kuma kula da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.