Rushe-rushe: Makaranta ta bayyana abin da ya sa aka rugurguza gidajen mutane 160 a Zaria

Rushe-rushe: Makaranta ta bayyana abin da ya sa aka rugurguza gidajen mutane 160 a Zaria

  • Nigerian College of Aviation Technology ta yi bayani a kan rushe-rushen da aka yi a Zaria
  • Makarantar NCAT tace filayen da ta karbe na ta ne tun shekaru kimanin 20 da suka wuce
  • Balarabe Mohammed yace ruguza gidajen zai samar da tsaro da kuma ayyukan yi a kasa

Kaduna - Makarantar nan ta NCAT ta koyar da tukin jirgin sama a Najeriya da ke garin Zaria, tayi karin haske a kan ruguza gidajen mutane da ta sa aka yi.

Leadership ta rahoto hukumar makarantar NCAT tana cewa ta dauki wannan matakin ne domin ta karbe filayen ta, ta hana mutane ratso mata cikin haraba.

Jami’in hulda da jama’a na makarantar tukin jirgin saman, Balarabe Mohammed ne ya fitar da jawabi kan batun a ranar Laraba, 6 ga watan Oktoba, 2021.

Read also

2023: Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Moghalu ya fice daga jam'iyyar YPP ya koma sabuwar jam'iyya

NCAT tace dama can filayen ta ne aka cinye

Jawabin yace an dauki sama da shekaru 20 mutanen garin Zaria suna cin filin makarantar.

“Hakan zai taimaka wajen kokarinmuu na zama daya daga cikin makarantar koyon jirgin saman da ya fi kowane kyau, kuma ya bada damar karatu da kyau.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kaduna
Hoton wasu gidaje da aka rusa a wata kasa Hoto: lassiterexcavating.com
Source: UGC

Malam Balarabe Mohammed yace hukumar ICAO ta Duniya ta kara wa NCAT matsayi, a dalilin haka za a bukaci babban fili na tashi da saukar jiragen sama.

Za a ga amfanin ruguza gidajen - NCAT

Mohammed a madadin NCAT ya bayyana yadda karbe filayen zai taimaka wa Zaria da kasa baki daya.

“Za a rika amfani da makarantar NCAT wajen neman kudi, ba koyar da tukin jirgi kawai. Hakan zai yi sanadiyyar samar da ayyukan yi a kasa baki daya.”

Har ila yau, jaridar ta rahoto Mohammed yana cewa ruguza gidajen da suka rabi makarantar zai taimaka wajen magance matsalar tsaro a kewayen kwalejin.

Read also

Katsina: ‘Yan sanda sun kama tsohuwar ma’aikaciyar hukumar NIS bisa damfara ta N47m

“NCAT ta gode wa hukumar KASUPDA da gwamnatin Kaduna da taimako da gudumuwar da ta ba mu wajen karfe filayenmu da aka ci na tsawon shekaru.”

Rusau a unguwar Grace land, Zaria

Kwanakin baya ku ka samu labari cewa gwamnati za ta rusa gidaje da gine-ginen al'umma a unguwar da ake kira Graceland da ke karamar hukumar Sabon Gari.

Wannan unguwa tayi makwabtaka da makarantar koyon tukin jirgin sama da ke hanyar Samaru, ana zargin filayen unguwar sun shiga cikin harabar filin makarantar.

Source: Legit

Online view pixel