Shugaba Buhari ne ɗan siyasan da yafi kowane farin jini da Nagarta a wannan zamanin, Osinbajo

Shugaba Buhari ne ɗan siyasan da yafi kowane farin jini da Nagarta a wannan zamanin, Osinbajo

  • Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa shugaba Buhari na da duk wata nagarta da Najeriya ke bukata
  • A cewarsa, babu ɗan siyasar Najeriya da ya fi shugaba Buhari ƙaurin suna da nagarta a wannan zamanin da muke ciki
  • Osinbajo ya yi kira ga yan Najeriya dake ciki da wajen Najeriya su cigaba da kasancewa tsintsiya ɗaya

United Kingdom - Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, yace shugaban ƙasa Buhari shine ɗan siyasar Najeriya da ya yi ƙaurin suna a zamanin nan.

Osinbajo ya faɗi haka ne ya yin ganawarsa da manyan jami'ai a ofishin jakadancin Najeriya na ƙasar Birtaniya, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Mataimakin shugaban yace ƙaurin suna da kuma nagartar shugaba Buhari, sune manyan ginshikan da ake bukata wajen kawo ƙarshen ƙalubalen kasar nan.

Kara karanta wannan

Halin da yan bindiga suka jefa mutane tun bayan katse hanyoyin sadarwa a jihar Katsina

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari
Shugaba Buhari ne ɗan siyasan da yafi kowane kaurin suna a wannan zamanin, Osinbajo Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Farfesa Osinbajo yace:

"Watakila shugaba Buhari shine ɗan siyasa a Najeriya da yafi kowanne ƙaurin suna a wanna zamanin."
"Shine wanda zai je wuri ba tare da ya kira mutane ba, su dakansu zasu zo sauraron jawabin da zai yi. Muna bukatar irin wannan nagartar wajen warware matsalolin ƙasar mu."
"Sabida nagartarsa, duk da abinda ke faruwa a yanzu, shi kaɗai ne zai kirayi kowa, ko da kuwa basa goyon bayansa, amma sun sani cewa shi mutum ne mai faɗa da cikawa."

Kada mu kuskura mu raba ƙasar mu - Osinbajo

Mataimakin shugaban ya kuma kirayi yan Najeriya a kan kada su kuskura a raba ƙasar nan, inda yake cewa a halin yanzun ƙananan ƙasashe na faɗi tashin haɗa kai da wasu domin su zauna da gindinsu.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, ya sake magana kan shirinsa na takarar shugaban ƙasa a 2023

"Ko ina kaje a faɗin duniyar nan, mutane na kokarin haɗa kawunan su wuri ɗaya, basu son rabuwa, bai kamata mu bari a raba Najeriya ba a yanzun."
"Idan ka duba tattalin arzikin ƙananan ƙasashe, zaka ga cewa suna neman hanyoyin ƙara ƙarfi ne ta hanyar haɗa kai da wasu."

Mataimakin shugaban ya yi kira ga yan Najeriya dake ƙasashen waje da kuma waɗanda ke zaune a cikin gida, su cigaba da kasancewa a dunƙule, kamar yadda this day ta ruwaito.

A wani labarin kuma Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, ya sake magana kan shirinsa na takarar shugaban ƙasa a 2023

Jega ya faɗi hakane a wurin wata lakca da yan Kwara suka shirya ranar Asabar, yace bai faɗawa kowa yana da sha'awar neman muƙamin shugaban ƙasa ba.

Ya kuma yi kira ga yan Najeriya da su tuhumi yan siyasar da suka zaba kan duk abinda suke fama da shi.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Jami'an Kwastam sun sake bude wuta kan jama'a a jihar Katsina

Asali: Legit.ng

Online view pixel