Yadda mata ke amfani da Hijabi wajen safarar muggan makamai ga yan fashi a Najeriya
- Wasu mata biyu da jami'an yan sanda suka cafke sun bayyana yadda suke tallafawa yan fashi ta hanyar amfani da Hijabi
- Matan sun bayyana yadda suke ɗaukar bindigu AK-47 daga wani wuri a umarce su kai ta wani wuri
- Kakakin yan sandan ƙasar nan, Frank Mba, yace hukumar yan sanda zata ɗauki jami'ai mata domin dakile faruwar irin haka
Abuja - Wasu mata biyu da yan sanda suka damke, sun bayyana yadda suke amfani da Hijabi wajen safarar muggan makamai ga yan fashin daji, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Kakakin yan sanda na ƙasa, Frank Mba, a makon da ya gabata, ya bayyana wasu mutum 11 da jami'an suka damke, cikinsu harda mata guda biyu.
Ɗaya daga cikin matan, Aisha Ibrahim, yar shekara 30, ta zayyana yadda ta ɗauki bindiga AK-47 daga Lafia, jihar Nasarawa zuwa Kaduna.
Aisha ta bayyana cewa ta samu nasarar kaiwa mutumin da aka aike ta wurinsa, wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda aka kama mai suna Babangida.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Hakanan kuma ɗayar matar da yan sandan suka cafke, Hafsat Adamu, tace ta ɗauki bindiga daga Kujama zuwa Abuja Junction dake cikin garin Kaduna.
"Na shiga motar haya, na ɓoye bindigar a cikin wani akwati. Adamu ne ya bani bindigar a Kujama kuma ya tarbe ni a Abuja Junction, daga nan muka rankaya zuwa Gwagwalada Abuja."
Muna samun sauki idan muka saka kakin soja
Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi, Musa Ibrahim, ya bayyana cewa idan suka yi amfani da kakin sojoji, suna samun sauki wajen satar mutane.
Ya kuma kara da cewa tawagarsu na gudanar da aikinta ne a Gwagwalada a Abuja, Kachia da Doba a jihar Kaduna.
Wane mataki yan sandan suka ɗauka?
Kakakin yan sanda, Frank Mba, yace hukumar yan sanda zata samar da jami'ai mata domin su rinka binciken yan uwansu mata.
Ya kuma roki yan Najeriya da su cigaba da baiwa jami'an yan sanda haɗin kai yayin da suke kokarin sauke nauyin dake kansu.
A wani labarin na daban mun kawo muku Halin da yan bindiga suke jefa mutane tun bayan katse hanyoyin sadarwa a jihar Katsina
Duk da matakan da gwamnatin jihar Katsina ta ɗauka, mazauna jihar sun fara kokawa kan yawaitar ayyukan yan bindiga.
A cewar mazauna ƙaramar hukumar Faskari, yan bindiga na cigaba da cin karensu babu babbaka.
Asali: Legit.ng