Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC ta lallasa PDP, ta lashe kujerun Ciyamomi da Kansiloli a jihar Filato
- Jam'iyyar APC mai mulki ta lashe baki ɗaya kujerun da aka fafata a kansu a zaɓen kananan hukumomi na jihar Filato
- Hukumar zaɓen jihar, (PLASIEC), ta bayyana cewa APC ta lashe kujerun ciyamomi 17 da kansiloli 325
- Gwamna Simon Lalong na jihar Filato, ya nuna jin daɗinsa bisa yadda hukumar zaɓe ta gudanar da aikinta lami lafiya
Plateau - Jam'iyyar APC ta lashe kujerun ciyamomi 17 a zaɓen kananan hukumomin da ya gudanar ranar Asabar a Filato.
Hakanan kuma Dailytrusr ta rahoto cewa APC ta lashe kujerun kansiloli 325 dake faɗin ƙananan hukumomi 17 a jihar.
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Filato (PLASIEC), Fabian Ntung, shine ya sanar da sakamakon zaɓen ranar Lahadi da safe.
Wane ƙalubale aka samu yayin zaɓen?
Rahotanni sun bayyana cewa mutane ba su damu da yin zaɓen ba kuma basu fito runfunan zaɓe don kaɗa kuri'unsu.
Wanna dai bai rasa nasaba da rashin hammayya a zaɓen, kasancewar jam'iyyar PDP ba ta shiga zaɓen ba saboda hukuncin kotu.
Kotu tace jam'iyyar PDP ba ta bi ƙa'idoji da dokoki ba wajen gudanar da zaɓen fidda ɗan takara, hakan ya saukaka wa APC.
A halin yanzun kotu ta zaɓi watan Nuwamba, domin sauraron ɗaukaka karar PDP na ƙalubalantar hukuncin hana ta shiga zaɓen.
Lalong ya yaba wa hukumar zaɓe
Gwamnan Filato, Simon Lalong, ya yaba wa hukumar zaben jihar, bisa yadda ta gudanar da zaɓen cikin nasara kuma babu tashin-tashina.
Ya ƙara da cewa yaji daɗin yadda mutane suka fito da gwarin guiwarsu wajen zaɓen shugabannin msu a gundumarsa, kamar yadda The nation ta ruwaito.
A wani labarin na daban Kotu ta tsige shugabannin kananan hukumomi 16 na APC da gwamna ya naɗa a wannan jihar
Babbar kotu ta yanke hukuncin rushe shugabannin riko da gwamnan Kwara ya naɗa a kananan hukumomi 16 na jihar.
Kotun tace babu dalilin da zai sa gwamna ya rushe zababbun ciyamomi, kuma ya maye gurbinsu da kantomomi.
Asali: Legit.ng