Tsohon shugaban INEC, Attahiru Jega, ya sake magana kan shirinsa na takarar shugaban ƙasa a 2023
- Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa sam bai taɓa tunanin tsayawa takarar shugaban ƙasar Najeriya a 2023 ba
- Tsohon shugaban hukumar zaɓe INEC yace ya yi imani da Allah, kuma ba abinda ya gagari Allah, saboda haka ya barwa Allah komai
- Jega ya yi kira ga yan Najeriya da su tuhumi yan siyasar da suka zaba kan duk abinda suke fama da shi
Abuja - Tsohon shugaban hukumar zaɓe (INEC), Farfesa Attahiru Jega, yace sam bashi da shirin neman kujerar shugaban ƙasa a 2023, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Jega ya faɗi hakane a wurin wata lakca da yan Kwara suka shirya ranar Asabar, yace bai faɗawa kowa yana da sha'awar neman muƙamin shugaban ƙasa ba.
Farfesa Jega yace:
"Ban faɗa wa kowa cewa inada da sha'awar tsayawa takarar shugaban ƙasa ba, jita-jita ce da raɗe-raɗin kafafen watsa labarai."
"Eh, gaskiya ne na yi rijista da jam'iyyar siyasa, saboda na yanke hukuncin cewa ba zan tsaya ina zuba ido ba kawai, zan bada tawa gudummuwar a siyasar Najeriya."
"Akwai lokacin komai amma a yanzun bani da shirin takara. Ni musulmi ne, na yi imani da Allah kuma nasan cewa ba abinda ya gagari Allah, saboda haka na barwa Allah komai."
Wasu mutane dake cikin gwamnatin ba su san komai ba- Jega
Farfesa Jega ya ƙara da cewa mafi yawan mutanen dake cikin gwamnati a yanzun ba su san hanyar warware ƙalubalen ƙasar nan ba.
Saboda haka, tsohon shugaban INEC ya yi kira ga yan Najeriya su tuhumi yan siyasa kan duk abinda ke faruwa, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Da duminsa: 'Yan daba sun yi wa babban jami'in APC duka har ya gigice, sun kona gidansa a jihar Nasarawa
Wace jam'iyyar siyasa Jega ya shiga?
Tun a shekarar 2019, tsohon shugaban hukumar zaɓe kuma kwararre a ilimin siyasa ya bayyana shigarsa jam'iyyar PRP.
Hakanan kuma a watan Satumba, 2021, Jega yana daga cikin waɗanda aka bayyana a sabuwar jam'iyyar da zata ceto Najeriya daga halin da ta shiga.
Wasu ƙungiyoyi da dama dake nuna goyon bayansu ga Attahiru Jega, sun yi kira gareshi da ya nemi takarar shugaban ƙasa a 2023.
A wani labarin na daban kuma kun ji cewa Kotu ta tsige shugabannin kananan hukumomi 16 na APC da gwamna ya naɗa a wannan jihar
Kotun tace babu dalilin da zai sa gwamna ya rushe zababbun ciyamomi, kuma ya maye gurbinsu da kantomomi.
Jam'iyyar adawa PDP ta bayyana jin daɗinta kan matakin kotun, inda tace wannan nasara ce ga mulkin demokaraɗiyya.
Asali: Legit.ng