Da duminsa: 'Yan daba sun yi wa babban jami'in APC duka har ya gigice, sun kona gidansa a jihar Nasarawa
- Lauyan APC a unguwar Wakama, Nasarawa, Waziri Enwongulu, ya tsallake rijiya da baya a ranar Asabar, 9 ga watan Oktoba
- Enwongulu ya ce wasu gungun ‘yan daba dauke da makamai ne suka kai masa hari a gidan dan uwansa da ke jihar a ranar Asabar
- Mai ba jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a ya bayyana cewa 'yan daba sun alakanta shi da wani laifin zabe a jihar
‘Yan daba sun kusa kashe lauyan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a gundumar Wakama, jihar Nasarawa, Waziri Enwongulu, a ranar Asabar, Oktoba.
Da yake fadawa jami'an APC mawuyacin halin da ya shiga a ranar Asabar, Enwongulu ya bayyana cewa miyagun sun je gidan ɗan'uwansa inda yake da zama sannan suka yi masa dukan tsiya.
Lauyan jam'iyyar ya bayyana cewa 'yan barandan sun yi iƙirarin cewa jam'iyyar ta yi magudi a sakamakon zaɓen ciyaman da na kansila a mazabar, don haka ne suka kai hari, kamar yadda PM News ta rahoto.
Ya kara da cewa baya ga kai masa farmaki, 'yan daban, kimanin su hudu dauke da wukake, adduna, da manyan sanduna, sun kona gidan dan uwan nasa.
Enwongulu ya ba da labari:
“A yau da misalin ƙarfe 1:10 na tsakar dare na ji wasu muryoyi a ƙofata cewa ya kamata in fito ko su ƙone gidan yayana har da ni.
“Lokacin da na fito daga gidan, sai na ga mutane hudu dauke da wukake, adduna da manyan sanduna. Sun shaida min cewa APC ta canza sakamakon zaben ciyaman da na kansila a gundumar Wakama.
“Sun nemi in kwanta kuma na yi biyayya, sannan kuma suka yi mun duka har na gigice. Lokacin da na kwanta, mutum biyu daga cikin mutanen sun yi gadina yayin da sauran biyun suka tafi suka sanyawa gidan babban yayana (Mista Paul Angbazo) da nake zaune wuta.”
Hukumar zaɓe ta sanar da sakamakon zaɓen kananan hukumomi 13 na jihar Nasarawa
A wani labarin, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe baki ɗaya kujerun da aka fafata a zaɓen ƙananan hukumomin jihar Nasarawa da ya gudana ranar Laraba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar, Ayuba Wandai, shine ya bayyana ne yayin da yake sanar da sakamakon zaɓen ranar Alhamis a Lafia, babban brinin jihar.
Wandai yace jam'iyyar APC ta lashe kujerun ciyaman da na kansiloli a baki ɗaya kananan hukumomi 13 dake faɗin jihar Nasarawa.
Asali: Legit.ng