Ya kamata 'yan Najeriya su fahimci ilimin Buhari don gane tasirinsa, Minista

Ya kamata 'yan Najeriya su fahimci ilimin Buhari don gane tasirinsa, Minista

  • Minstan ayyuka da gidaje ya bayyana wasu kalamai masu bukatar tunani kan shugaba Buhari
  • Ya bayyana cewa, 'yan Najeriya basu fahimci wanene shugaban ba, shi yasa basu gane tasirinsa ba
  • Ya bayyana haka ne cikin wani shirin da aka watsa a gidan talabijin Channels a karshen mako

Ministan Ayyuka da Gidaje na Najeriya, Babatunde Fashola, ya ce dole ne 'yan Najeriya su san ilimi da horon da shugaban kasa Muhammadu ya samu don fahimtar tasirin sa kan mulki.

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin shiri mai taken, 'The Effect Buhari: Undeniable Achievements', wanda aka watsa a gidan Talabijin na Channels a yammacin Asabar 9 ga watan Oktoba.

Shirin na awa daya ya ba da labarin wasu “nasarori” na gwamnatin Buhari a duk fannonin shugabanci da suka hada da ci gaban ababen more rayuwa, gidaje, noma, sufuri, kiwon lafiya, da sauran su.

Kara karanta wannan

Ban taba ganin Shugaban kasa mai hakuri irin Shugaba Buhari ba, Lai Mohammed

Ya kamata 'yan Najeriya su fahimci ilimin Buhari don gane tasirinsa, Minista
Minstan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola | Hoto: guardian.ng
Asali: Depositphotos

Jaridar Punch ta rahoto Fashola, tsohon gwamnan Legas, na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Hanya mafi kyau don fahimtar tasirin Buhari shine fahimtar mutumin karan kansa da yaba alakar sa ta hanya mai sauki ga mafi rauni ga jama'ar mu.
"Hakanan don fahimtar asalin sa, ilimin sa da horon sa.
"Idan kuka koma baya kuka duba abin da ya gabata a cikin gwamnati, ko a matsayin matashin soja, a matsayin GOC (Babban Jami'in Umarni), ko a matsayin gwamnan soja ko a matsayin Ministan Man Fetur ko a matsayin Shugaban Amintaccen Asusun Man Fetur, za ku fahimci komai game da mutumin."

Cece-kuce kan batun karatun Buhari

An samu rigimar da ta dabaibaye takardun karatun shugaba Buhari kamar yadda jam’iyyar adawa ta PDP, a watan Oktoban 2018, ta kalubalanci Buhari da ya gabatar da takardun karatun sa “idan yana da su,” ga hukumar zabe ta INCE.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya koma APC a hukumance, ya gana da shugaban jam'iyyar a Abuja

An rahoto cewa Shugaban ya sanar da INEC cewa takardun sa na hannun hukumar soji.

Batutuwa kan ingancin takardun Buhari, duk da haka, ya ci gaba da haifar da cece-kuce daga masu sa ido a harkar siyasa.

Don kwantar wutar rikicin, hukumar jarrabawa ta WAEC, a Nuwamban 2018, ta gabatar da takardar da sakamakon kammala sakandare ga Buhari a wani hoto da aka yi ta yadawa.

Buhari, mai shekaru 78, tsohon shugaban kasa na mulkin soja tsakanin shekarar 1983 zuwa 1985, ya kasance zababben shugaban Najeriya na dimokuradiyya tun daga watan Mayun shekarar 2015.

Sai dai, ‘yan Najeriya da dama na ci gaba da kukan halin tabarbarewar tsaro, tattalin arziki, hauhawar farashin abinci, da hauhawar rashin aikin yi a karkashin ragamarsa.

Gwamnatin Buhari za ta fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa

A bangare guda, Gwamnatin Tarayya ta amince da biyan N75,000 a matsayin alawus-alawus na kowane semester ga daliban da ke karatun digiri a fannin Ilimi a jami'o'in gwamnati a Najeriya, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Buƙaci a Kama Musulmin Da Suka Kashe Fasto a Kano

Hakanan, daliban NCE za su karbi N50,000 a matsayin alawus na kowane semester a wani kokarin gwamnati don jawo hankalin samar da kwararrun malaman makaranta kamar yadda Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi alkawari shekaran da ya gabata.

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, ya sanar da hakan a ranar Talata 5 ga watan Oktoba, a bikin ranar malamai ta duniya da aka gudanar a Eagle Square da ke babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel