Labari da Hotuna: Jagoran APC Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan jinya a Landan

Labari da Hotuna: Jagoran APC Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan jinya a Landan

  • Jigon jam'iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, ya dawo Najeriya bayan fama da jinya a Landan
  • Tsohon gwamnan ya samu tarba daga gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, bayan isowarsa ranar Jumu'a da yamma
  • Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan kaddamar da yaƙin neman takararsa a babban zaɓen 2023 dake tafe

Lagos - Jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya dawo gida Najeriya bayan yi masa tiyata a birnin Landan na ƙasar Birtaniya.

The Cable ta rahoto cewa Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya dawo Najeriya ne ranar Jumu'a da yamma.

A wata sanarwa da kakakinsa, Tunde Rahman, ya fitar, ya bayyana cewa an yiwa tsohon gwamnan tiyata a guiwarsa ta dama.

Bola Tinubu
Labari da Hotuna: Jagoran APC Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan jinya a Landan Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wani sashin sanarwar tace:

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan daba sun yi wa babban jami'in APC duka har ya gigice, sun kona gidansa a jihar Nasarawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mai girma, Asiwaju Bola Tinubu, ya dawo kasa Najeriya, ya dira Legas da yammacin ranar Jumu'a, 1 ga watan Oktoba."
"A yayin tafiyarsa ƙasar waje, likitoci sun masa aiki a kafarsa ta dama. Babu wani aiki da aka masa bayan wannan kamar yadda ake yaɗa jita-jita."
"Ya dawo cikin gaggarumar nasara daga aikin da aka masa kuma zai cigaba da bada gudummuwarsa wajen tafiyar da kyakkyawar gwamnatin APC."

Tinubu ya gode wa shugaba Buhari

Jigon jam'iyyar APC, ya nuna matuƙar jin dadinsa da godiya ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da sauran masu rike da mukaman siyasa, waɗanda suka ziyarce shi lokacin da yake Landan.

Tinubu ya iso Najeriya ne awanni kaɗan bayan kaddamar da yakin neman takararsa a zaɓen 2023, wanda ya gudana Legas, kamar yadda The nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya koma APC a hukumance, ya gana da shugaban jam'iyyar a Abuja

Shin Tinubu ya amince da yin takara?

Har zuwa yanzun jigon jam'iyyar APC mai Mulki, Bola Tinubu, bai bayyana sha'awar neman takarar shugaban ƙasa ba da bakinsa.

Amma gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu, wanda ya tarbi Tinubu a filin jirgi, ya nuna goyon bayansa da lamarin.

Hotunan dawowarsa Najeriya

Jagoran APC Bola Tinubu
Labari da Hotuna: Jagoran APC Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan jinya a Landan Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Jagoran APC Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan jinya a Landan
Labari da Hotuna: Jagoran APC Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan jinya a Landan Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Bola Tinubu
Labari da Hotuna: Jagoran APC Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan jinya a Landan Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A wani labarin na daban kuma mun tattaro muku Jerin jihohi Najeriya 6 da zasu amfana da sabon tallafin COVID19 daga asusun NSSF

Asusun tallafi na NSSF ya baiwa hukumar lafiya a matakin farko NPHCDA gudummuwar miliyan N300m.

A cewar NSSF, tallafin zai taimaka matuka wajen yiwa yan Najeriya rigakafin COVID19 a wasu jihohin Najeriya shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262