'Yan bindiga sun kashe mutum 10, sun raunata wasu da dama a sabon harin da suka kai Katsina
- Yan bindiga sun kai sabon hari a garin Yasore da ke kusa da Batsari a jihar Katsina
- Yayin harin, sun bindige mutum 10 har lahira, sun raunata wasu sun kona gidaje
- Wani mazaunin garin ya tabbatar da afkuwar harin inda ya ce wadanda suka jikkata suna asibiti
Katsina - 'Yan bindiga a safiyar ranar Talata sun kashe mutum 10 sun kuma raunata wasu da dama yayin sabon harin da suka kai inda suka kona shaguna da gidaje a Yasore, jihar Katsina, mazauna garin suka shaidawa Premium Times.
Yasore ba shi da nisa da Batsari, hedkwatar karamar hukumar Batsari.
Batsari na daya daga cikin kananan hukumomin da 'yan bindiga ke yawan kai hari. Yana da iyaka da dajin Rugu, karamar hukumar Katsina da Zurmi a jihar Zamfara.
An toshe layukan sadarwa a Batsari da wasu kananan hukumomi 13 a jihar a matsayin wani mataki na magance 'yan bindiga.
Wani mazaunin unguwar, Harisu Hamsa, ya shaida wa Premium Times cewa maharan sun taho ne a kan babura suka fara harbe-harbe.
Ya ce:
"Sun taho lokacin sallar Magariba. Wasu sun gama salla a lokacin. Sun taho kan babura fiye da 20, a yayin harbe-harben ne suka kashe mutum 10 suka raunata wasu."
Mr Hamza wanda ke zaune a birnin Katsina ya tabbatar da cewa yan bindigan sun cinna wa wasu gidaje wuta.
A cewarsa:
"Sun sace kayan abinci da wasu kayayyakin da suke bukata a yayin harin."
Majiyar Legit.ng ta tattaro cewa an kai wadanda suka jikkata babban asibitin Katsina.
Mai magana da yawun yan sandan jihar, Gambo Isa, ya ce yana cikin taro ne a lokacin da wakilin majiyar Legit.ng ya tuntube shi. Amma, bai amsa sakon kar ta kwana da aka aika masa ba.
Sarkin Katsina ya barranta da matsayar Sheikh Gumi: Kisa ya dace da ƴan bindiga ba tattaunawa da su ba
A wani labarin daba, mai martaba Sarkin Katsina ya ce tunda ƴan bindiga sun zaɓi su rika kashe mutane 'suma bai dace a bar su da rai ba'.
Sarkin na Katsina, Abdulmuminu Usman ya ce ba abin da ya dace da ƴan bindigan da ke kashe mutane a arewa maso yamma illa kisa.
Sarkin ya yi wannan furucin ne yayin taron tsaro na masu ruwa da tsaki a ranar Talata a Katsina kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Asali: Legit.ng