Yadda 'yan bindiga suka afka wa wani gari a Sokoto yayin da suke neman sojoji

Yadda 'yan bindiga suka afka wa wani gari a Sokoto yayin da suke neman sojoji

  • ‘Yan bindiga sun afka kauyen Gangara bayan kwana 2 da suka harbe sojoji 17 a sansanin su dake Dama
  • Dan majalisar jihar na yankin, Sa’idu Ibrahim ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga su na harin jami’an tsaro ne a yankin
  • A cewarsa, ranar Talata sun shiga kauyen har sau biyu su na neman sojoji da basu same su ba suka fara harbe-harbe

Jihar Sokoto - ‘Yan bindiga sun afka Gangara, wani kauye dake karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto a ranar Talata, sun je kai wa sojoji farmaki.

‘Yan bindiga sun afka yankin ne bayan bai wuci sa’o’i 48 da suka harbe sojoji 17 a sansanin su da ke Dama ba, duk a karamar hukumar Sabon Birni kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke ma'aikacin jinyan MSF da wasu mutum 2 a Zamfara

Yadda 'yan bindiga suka afka wa wani gari a Sokoto yayin da suke neman sojoji
'Yan fashin daji. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dan majalisar jihar na yankin, Sa’idu Ibrahim ya ce yanzu ‘yan bindiga su na harin jami’an tsaro ne a yankin.

Ya ce a shirye suke da su kai sojoji maboyar ‘yan bindiga

A cewar sa su na boyewa ne a wani wuri da suke kira ‘Tudun Katsira’ da ke tsakanin

Bafarawa da Burkusuma inda ya kara da cewa:

“A shirye muke da mu raka jami’an tsaro har wurin.”

Kamar yadda dan majalisar ya bayyana ana harin wurin, inda yake cewa:

“Muna zaune ne cikin tsoron su, za su iya halaka mu duk lokacin da suka so, su suke fada mana abinda zamu yi su hana mu abinda suka ga dama. Babu wani shugaba da yake da ikon cewa komai sai abinda ‘yan bindiga suka ga dama suke yi mana.

Kara karanta wannan

‘Yan IPOB sun kashe tsohon Sarki, Mijin tsohuwar Minista da Direban ‘Dan Majalisa a wata daya

“Sun kai farmaki kauyen Gangara sau 2 a ranar Talata, sun fara zuwa ne karfe 5 na safe, da basu ga wani jami’in tsaron da za su halaka ba sai su ka tafi. Sun kara komawa karfe 3 na rana su na mana tsawa su na cewa ‘Ina sojojin da suke neman ganin bayan mu suke? Ina suke?’
“Da suka ga babu jami’an tsaro sai suka hau harbin mazauna kauyen.”

Yayin da aka nemi jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, ASP Sanusi Abubakar, ya bayyana cewa bai san komai ba dangane da farmakin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Hotunan Mutane 5 Masu Garkuwa Da Mutane Da Ƙwararrun Mafarauta Suka Kama a Kogi

A wani labarin daban, kwararrun mafarauta a karamar hukumar Okehi a jihar Kogi sun yi nasarar kama mutane biyar 'yan kungiyar masu garkuwa da mutane, LIB ta ruwaito.

An kama mutane biyar din da ake zargi a safiyar ranar Talata a Atami, wani gari da ke wajen Osara a ranar Talata, 27 ga watan Satumban shekarar 2021.

Kara karanta wannan

Ganduje, Amaechi, Ikweremadu, wasu mutum 22 da suke cin taliyar siyasa tun 1999 har yanzu

King Habib, babban hadimi ga shugaban karamar hukumar Okehi a bangaren watsa labarai, Hon Abdulraheem Ohiare Ozovehe ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, yana mai cewa tawagar sun dade suna adabar mutane a titin Okene-Lokoja da Okene-Auchi a jihar Kogi State.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel