Ya kamata 'yan Najeriya su dinga auren waɗanda ba ƙabilar su ɗaya ba, Rochas Okorocha

Ya kamata 'yan Najeriya su dinga auren waɗanda ba ƙabilar su ɗaya ba, Rochas Okorocha

  • Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya shawarci ‘yan Najeriya akan auren wadanda ba kabilar su daya ba
  • Kamar yadda Okorocha ya bayyana, hakan yana kara hadin kai da zaman lafiya a cikin kasa
  • Ya bayyana hakan ne a wani taro da kungiyar NICO ta shirya a ranar 7 ga watan Oktoba a jihar Kano

Jihar Kano - Rochas Okorocha, Sanatan jihar Imo ya shawarci ‘yan Najeriya akan auren wadanda ba kabilar su daya ba.

Kamar yadda The Sun ta ruwaito, Okorocha wanda yanzu haka sanata ne kuma tsohon gwamnan jihar Imo, ya ce akwai falalar yin hakan.

Ya kamata 'yan Najeriya su dinga auren wadanda ba ƙabilar su ɗaya ba, Rochas Okorocha
Sanata Rochas Okorocha. Hoto: Daily Trust

Read also

An samu jihar Kudancin Najeriya da tayi doka, ta haramta saida giya a tashar motoci

A cewar sa, auratayya tsakanin kabilu ya na kara dankon so, zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa.

Ya bayyana hakan ne a wani taro da ya shugabanta wanda ake yi duk shekara don samar da hadin kan kabilu wanda cibiyar wayar da kai akan kabilu ta Najeriya (NICO) ta shirya, inda ya ce hakan hanyar samar da hadin kan ‘yan Najeriya ne kamar yadda The Sun ta ruwaito.

A cewar sa akwai kabilu fiye da 200 a Najeriya

Okorocha wanda ya samu wakilcin Farfesa Sunny Ododo, a ranar Litinin 7 ga watan Oktoba a jihar Kano ya ce akwai yaruka fiye da 400 a Najeriya da kabilu fiye da 200.

Don haka wajibi ne samar da zaman lafiya tsakanin su.

Okorocha wanda shi ne shugaban kwamitin al’adu a majalisar tarayya ya ce gwamnatin tarayya ta na iyakar kokarin ganin ta samar da hadin kai tsakanin kabilu ta hanyar amfani da bautar kasa (NYSC).

Read also

Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Buƙaci a Kama Musulmin Da Suka Kashe Fasto a Kano

Sannan ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed, wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar wayar da kai ta kasa, Lawal Haruna ya ce ya kamata mu yi amfani da damar mu ta bambancin al’adu wurin bunkasa zaman lafiya da samar da ci gaba a kasar mu.

Dole ciki ya sa ki saduda da rayuwa, hotunan yadda juna biyu ya sauya wa wasu mata hallita

A wani labarin daban, mata da dama su na fuskantar canji a jikin su yayin da suke dauke da juna biyu, wasu su na yin haske yayin da wasu suke yin duhu kwarai. Akwai wadanda suke yin kiba sosai wasu kuma su rame.

Akwai matan da suke yin kyau ko a fuska yayin da wasu kuma kureje suke bayyana musu duk su canja.

Ba rashin gyara ne yake kawo hakan ba, ba kuma talauci ko kuncin rayuwa ba, hakanan ciki yake mayar da mata kuma abin a hankali ne yake faruwa.

Source: Legit.ng

Online view pixel