An samu jihar Kudancin Najeriya da tayi doka, ta haramta saida giya a tashar motoci
- Hope Uzodinma ya kafa majalisar da za ta rika kula da hanyoyi a jihar Imo
- Gwamnan ya kuma bada umarnin a dakatar da tallar giya a tashoshin mota
- Gwamnatin Imo tana sa rai hakan zai taimaka wajen rage aukuwar hadura
Imo - Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma ya haramta saida giya da duk wasu na’ukun lemu masu sa maye a tasoshin mota a fadin jihar.
A ranar Alhamis, 7 ga watan Oktoba, 2021, ABN TV ta fitar da rahoto cewa Mai girma gwamna Hope Uzodinma ya bada wannan umarni a Owerri.
Rahoton yace Gwamnan na jihar Imo ya bayyana hakan ne wajen kaddamar da majalisar da ya kafa domin ta rika bada shawara a kan harkar tituna.
Gwamna Uzodinma yace majalisar da ya kafa za ta maida hankali kan abubuwa biyar; kula da tituna, samar da matafiya masu tuki a tsanake.
Haka zalika majalisar za ta bada karfi wajen ganin an dauki matakin gaggawa bayan aukuwar hadura, tare da samar da tituna masu nagarta a jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Meyasa za a daina saida giya a tasha?
Hope Uzodinma yace makasudin yin hakan shi ne a rage aukuwar haduran mota daga kashi 50% zuwa tsakanin kashi 20% da kuma 30% a titunan Imo.
A cewar gwamnan, ana yawan fama da haduran mota a hanyoyin jihar Imo, don haka ya sa dokar.
A jawabinsa, Hope Uzodinma ya bayyana irin kokarin da gwamnatinsa take yi wajen rage hadura da kuma ganin matafiya sun ji dadin bin titunan Imo.
Uzodinma yace kokarin rage aukuwar hadura a manyan hanyoyi ne ya sa gwamnatinsa ta bada kwangilar fadada titunan Owerri-Orlu da Owerri-Okigwe.
Fadada wadannan manyan tituna zai bunkasa tattalin arzikin jihar Imo, a cewar Sanata Uzodinma.
Wannan mataki da gwamnatin Uzodinma ta dauka ya jawo surutu a dandalin Nairaland. Wasu suna sukar gwamnan da cewa yana kokarin kawo shari'a.
Za mu karasa ayyukan da muke yi - Buhari
A ranar Alhamis, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za tayi kokari ta kaddamar da ayyukan da ta tattago.
Da yake gabatar da kasafin kudin 2022 a majalisa, Buhari yace kwanan nan za a fara aikin jirgin kasan Ibadan zuwa Kano, da na Fatakwal zuwa Maiduguri.
Asali: Legit.ng