Dole ciki ya sa ki saduda da rayuwa, hotunan yadda juna biyu ya sauya wa wasu mata hallita

Dole ciki ya sa ki saduda da rayuwa, hotunan yadda juna biyu ya sauya wa wasu mata hallita

  • Mata da dama su na fuskantar canji na surar su yayin da suke da juna biyu
  • Wasu baya ga kiba da suke yi a jikin su, har fuskar su da launin fatar su na canjawa
  • Hotunan yadda ciki ya mayar da mata da dama, ciki har da jaruman fina-finai

Mata da dama su na fuskantar canji a jikin su yayin da suke dauke da juna biyu, wasu su na yin haske yayin da wasu suke yin duhu kwarai.

Akwai wadanda suke yin kiba sosai wasu kuma su rame. Akwai matan da suke yin kyau ko a fuska yayin da wasu kuma kureje suke bayyana musu duk su canja.

Dole ciki ya sa ki saduda da rayuwa, hotunan yadda juna biyu ya sauya wa wasu mata hallita
Hotunan yadda juna biyu ya sauya kamanin mata. Hoto: #pregnancyhumbledme
Source: Instagram

Ba rashin gyara ne yake kawo hakan ba, ba kuma talauci ko kuncin rayuwa ba, hakanan ciki yake mayar da mata kuma abin a hankali ne yake faruwa.

Read also

Sokoto: Yadda ƴan bindiga suka amshe miliyoyi daga basarake kuma suka ƙi sako waɗanda suka yi garkuwa da su

Mata da dama sun yi ta wallafa hotunan yadda ciki ya mayar da su, ciki har da fitattun jaruman fina-finai kamar yadda suka wallafa a shafukansu na instagram.

Dole ciki ya sa ki saduda da rayuwa, hotunan yadda juna biyu ya sauya wa wasu mata hallita
Hoton yadda ciki ya canja kamanin mata. Hoto: #pregnancyhumbledme
Source: Instagram

Ba ya ga canji a surar su, har launin fatar su da fuskar su duk su na canjawa.

Dole ciki ya sa ki saduda da rayuwa, hotunan yadda juna biyu ya sauya wa wasu mata hallita
Hoton yadda ciki ya canja surar mata. Hoto: #pregnancyhumbledme
Source: Instagram

Ciki ya sauya mu su halittar su

Mata da dama sun wallafa hotunan su yayin da suke da juna biyu a kafafen sada zumunta dauke da taken #PregnancyWillHumbleYou da kuma #PregnancyHumbledMe, ma’ana ‘Ciki zai sa ki saduda da kuma ciki ya sa na saduda.

Bisa yadda ta ruwaito a Instagram, mai gabatar da shirye-shirye a rediyo, Tolu Oniru-Demuren wacce aka fi sani da Toolz da kuma jaruma Toyin Abraham ma sun shiga jerin masu wallafa hotunan, inda su ka bayyana yadda cikin ya mayar da su.

Read also

Kada ka damu kan ka, ƴan Najeriya ba su cancanci taimako ba, Jaruma Ruth Kadiri

Hotunan wani mutum da ya auri tukunyarsa ta dafa shinkafa ya ɗauki hankulan mutane

A wani labarin daban, kun ji wani mutum dan asalin kasar Indonesia ya janyo cece-kuce bayan ya bayyana yadda shagalin auren sa da tukunyar girkin lantarkin sa ya kasance.

Kamar yadda ya wallafa hotunan bikin, ya na sanye ne da fararen kaya na alfarma yayin da tukunyar take lullube da mayafi irin na amare kamar yadda LIB ta ruwaito.

Khoirul Anam ya wallafa hotunan a shafin sa na Facebook inda ya bayyana cewa an daura auren sa da tukunyar girkin lantarkin tun ranar 20 ga watan Satumba kamar yadda LIB ta ruwaito.

Source: Legit.ng

Online view pixel