Hukumar INEC ta saki jerin sunayen yan takaran zaben gwamnan Anambra 18

Hukumar INEC ta saki jerin sunayen yan takaran zaben gwamnan Anambra 18

Ana sauran wata daya daidai da zaben gwamnan jihar Anambra, hukumar shirya zaben kasa mai zaman kanta (INEC) ta saki sunayen yan takaran zaben na karshe.

Legit ta tattaro cewa a wannan jerin sunaye na karshe, hukumar ta sanya sunan Valentine Chineto Ozigbo matsayin dan takaran jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Zaku tuna cewa a jerin sunayen da INEC ta saki a baya, jam'iyar PDP bata da dan takara saboda rikice-rikicen kotu.

Hukumar INEC ta saki jerin sunayen yan takaran zaben gwamnan Anambra 18
INEC ta saki jerin sunayen yan takaran zaben gwamnan Anambra 18 Hoto: INEC
Asali: UGC

Festus Okoye, shugaban kwamitin labarai da wayar da kan jama'a a jawabin da ya saki a shafin Facebook cewa jam'iyyun siyasa 18 zasu yi takara a zaben 6 ga Nuwamba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga jerin yan takaran da INEC ta saki:

Kara karanta wannan

Manchester City, Juventus, Chelsea, da Jerin masu kulobs 7 mafi dukiya a shekarar 2021

1. Ekene Alex Nwankwo (Jam'iyyar Accord A)

2. Doreen Ifeoma Madukaarisa (Jam'iyyar Action Alliance, AA)

3. Obi Sylvester Chukwudozie (Jam'iyyar African Action Congress, AAC)

4. Akachukwu Sullivan Nwankpo (Jam'iyyar African Democratic Congress, ADC)

5. Prince Ume-Ezeoke Afam Luke Douglas (Jam'iyyar Action Democratic Party, ADP)

6. Emmanuel Andy Nnamdi Uba (Jam'iyyar All Progressives Congress, APC)

7. Chukwuma Michael Umeoji (Jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA)

8. Eze Robinson Chukwuma (Jam'iyyar Allied Peoples Movement, APM)

9. Azubuike Philip Echetebu (Jam'iyyar Action Peoples Party, APP)

10. Chika Jerry Okeke (Jam'iyyar Boot Party, BP)

11. Agbasimalo Obiora Emmanuel (Jam'iyyar Labour Party, LP)

12. Ohajimkpo Leonard Emeka (Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP)

13. Adaobi Uchenna Okpeke (Jam'iyyar National Rescue Movement, NRM)

14. Valentine Chineto Ozigbo (Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP)

15. Nnamdi Nwawuo (Jam'iyyar Peoples Redemption Party, PRP)

16. Ekelem Edward Arinze (Jam'iyyar Social Democratic Party, SDP)

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya dira jihar Kaduna don halartan bikin yaye daliban makarantar Soji NDA

17. Ifeanyi Patrick Ubah (Jam'iyyar Young Progressive Party, YPP)

18. Ugwoji Martin Uchenna (Jam'iyyar Zenith Labour Party, ZLP)

Hukumar INEC ta saki jerin sunayen yan takaran zaben gwamnan Anambra 18
Hukumar INEC ta saki jerin sunayen yan takaran zaben gwamnan Anambra 18
Asali: UGC

Gwamnatin Shugaba Buhari ta yi barazanar kafa dokar ta baci a wannan jihar

A ranar Laraban, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata iya kafa dokar ta baci a jihar Anambra idan akwai bukatar hakan, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

A cewar gwamnatin shugaba Buhari, zata ɗauki duk matakin da ya dace domin tabbatar da an gudanar da zaɓen 6 ga watan Nuwamba a jihar.

Antoni Janar, Abubakar Malami, shine ya faɗi haka yayin da yake amsa tambayoyin manema labari jim kaɗan bayan taron FEC a fadar shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel