Shugaba Buhari ya dira jihar Kaduna don halartan bikin yaye daliban makarantar Soji NDA
- Shugaba Buhari ya tafi Kaduna don halartan biki gobe Asabar
- Gwamnan jihar Kaduna tare da mukarrabansa sun tarbi shugaban kasan
- Kowace shekara ana yaye dalibai a jami'ar kuma Buhari na zuwa ko a wakilcesa
Kaduna - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dira jihar Kaduna ranar Juma'a domin halartan bikin yaye daliban jami'ar horar da Sojojin Najeriya, NDA, da aka shirya ranar Asabar, 9 ga Oktoba, 2021.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook da yammacin Juma'a.
A riwayar Leadership, Jirgin Shugaban kasan ya dira barikin Sojin sama dake Mando Kaduna ne daidai karfe 4:40.
Shugaban kasa ya samu rakiyar Ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi, dss.
Ya samu kyayyawan tarba daga wajen gwamna Nasir El-Rufa'i tare da manyan jami'an gwamnatin jihar Kaduna.
Hakazalika manyan hafsohin Sojin Najeriya fari da Janar Lucky Irabor; babban hafsan Sojin kasa, Laftanan Janar Farouq Yahaya; Babban hafsan sojin sama, Air Marshall Isiaka Amao, da kuma Vice Admiral Awwal Gambo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rundunar soji ta kai farmaki sansanin ‘yan bindiga, ta ceto babban sojan da aka sace a NDA
Zaku tuna cewa kwanakin baya yan bindiga sun kai hari makarantar Soji NDA inda suka kashe Soji kuma sukayi garkuwa da Manjo guda.
Manjo CL Datong, wanda aka yi garkuwa da shi lokacin da 'yan bindiga suka kutsa NDA a Kaduna, a watan da ya gabata, ya samu kubuta.
An kashe manyan jami’an biyu a lamarin wanda ya faru a ranar 24 ga Agusta, 2021.
A daren Juma'a, 17 ga watan Satumba, Mataimakin Daraktan Hulda da Jama'a na Runduna ta 1, Sojojin Najeriya, Kanal Ezindu Idimah, ya ce sojoji sun ceto Datong, jaridar Punch ta ruwaito.
Ya ce ayyukan da suka kai ga kubutar da shi sun kai ga rusa sansanonin ‘yan ta’adda da aka gano a yankunan Afaka- Birnin Gwari na jihar.
Asali: Legit.ng