Babbar Magana: Gwamnatin Shugaba Buhari ta yi barazanar kafa dokar ta baci a wannan jihar
- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar kafa dokar ta baci a jihar Anambra domin tabbatar da an gudanar da zaɓen gwamna
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta shirya gudanar da zaɓe a jihar Ranar 6 ga watan Nuwamba, 2021
- Ministan shari'a, Abubakar Malami, yace gwamnatin tarayya ta shirya aiwatar da komai da ya dace don tabbatar da an baiwa mutane haƙƙinsu
Abuja - A ranar Laraban nan, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata iya kafa dokar ta baci a jihar Anambra idan akwai bukatar hakan, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
A cewar gwamnatin shugaba Buhari, zata ɗauki duk matakin da ya dace domin tabbatar da an gudanar da zaɓen 6 ga watan Nuwamba a jihar.
Antoni Janar, Abubakar Malami, shine ya faɗi haka yayin da yake amsa tambayoyin manema labari jim kaɗan bayan taron FEC a fadar shugaban ƙasa.
Bugu da ƙari, Malami yace ba abinda gwamnati ba zata yi ba wajen tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.
Me FG ta shirya yi domin zaɓen Anambra?
Dailytrust ta rahoto Ministan shari'a, Malami, yace:
"Matukar aka farmaki tsaron mu na ƙasa, kuma muka samu barazana a demokaraɗiyya, to zamu yi duk abinda ya dace."
"A matsayin mu na gwamnati, haƙƙin mu ne tabbatar da bin doka da oda kuma hakkin mu ne tsare rayuwar al'umma da dukiyoyinsu."
"Saboda haka, bisa waɗannan nauye-nauye da kundin tsarin mulki ya ɗora mana, ba hanyar da ta dace da bazamu bi ba."
Zamu yi duk abinda ya dace - Malami
Ministan ya kara da cewa gwamnati ta shirya yin duk abinda ake bukata domin tabbatar an gudanar da zaɓen gwamnan jihar Anambra.
"Ba abinda ba zamu iya ba, har da kafa dokar ta baci. Saboda haka matsayar mu a gwamnatance shine zamu samar da jami'an tsaro domin tabbatar da an yi zaɓen."
A wani labarin kuma Wanda ya dace APC ta tsayar ya gaji shugaba Buhari a zaɓen 2023, Tsohon Minista ya magantu
Tsohon minista a Najeriya, Adeseye Ogunlewe, ya bayyana cewa jigon APC, Bola Tinubu, shi ne ya fi cancanta ya gaji shugaba Buhari a 2023.
Ogunlewe ya bayyana cewa a ranar Alhamis mai zuwa za'a ƙaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu reshen mahaifarsa, jihar Legas.
Asali: Legit.ng