Bollywood: An Kama Ɗan Shahararren Jarumi a Masana'antar Shirya Fina-Finan India

Bollywood: An Kama Ɗan Shahararren Jarumi a Masana'antar Shirya Fina-Finan India

  • Rahotanni na nuni da cewa hukumomin tsaro sun cafke ɗan shahararren jarumin Bollywood, Shah Rukh Khan, wato Aryan Khan
  • Khan ya shiga hannun jami'an hukumar NCB ne bisa zarginsa da shan miyagun kwayoyi a lokacin wata liyafa
  • Hakanan kuma an damke ɗan karamin ministan cikin gida, Ashish Mishra, da zargin bada umarnin take wasu manoma da mota

India - Rahotanni dake fitowa daga ƙasar Indiya, sun nuna cewa hukumomi sun cafke, Aryan Khan, ɗan shararren jarumi, Sharukh Shah Rukh Khan, ranar Lahadi.

BBC Hausa ta ruwaito cewa jami'an hukumar (NCB), masu sanya ido kan masu shan miyagun kwayoyi, sun damƙe Aryan Khan ne bisa zarginsa da shan miyagun kwayoyi yayin wata liyafa ta nishaɗi.

Khan ya shiga hannu ne yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Goa daga Mumbai, tare da iyalansa a cikin wani jirgin ruwa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sojoji sun sako shahararren jarumin Nollywood da suka damke

Aryan Khan
Bollywood: An Kama Ɗan Shahararren Jarumi a Masana'antar Shirya Fina-Finan India Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Meyasa aka tsare Aryan Khan?

Jami'an hukumar NCB, da suka jagoranci damke Aryan Khan, sun bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne ƙarƙashin doka, "Mai alaka da sha da fataucin miyagun kwayoyi."

Masana dake sharhi kan al'umaran dake faruwa yau da kullum, na ganin cewa yawan kwayoyin da aka kama shi da su basu kai a tsare shi ba.

Hakanan masu sharhin na ganin cewa babu wani kwakkwaran dalili na tsare Khan duba da takardun da suka bayyana na cafke shi.

Hukumomi sun kama ɗan minsita a Indiya

Hakazalika, hukumomi a ƙasar ta Indiya sun cafke ɗan ƙaramin ministan cikin gida, Ashish Mishra, bisa zargin baiwa direbansa umarnin taka manoma dake zanga-zanga.

Lamarin dai ya haddasa mutuwar wasu daga cikin mutanen dake zanga-zangar, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe yan sanda, Lauyoyi tare da kona fasinjojin wata mota

A wani labarin na daban Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

Kakakin yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, yace mutanen sun ce, suna zargin shugaban CAN da ɓoye wani mai laifi.

Rahoto ya nuna cewa Fasto Yohanna, ya jefa kanshi a cikin lamarin wani mutumi da mutane ke zargi da hallaka matar yayansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262