Da Duminsa: Sojoji sun sako shahararren jarumin Nollywood da suka damke

Da Duminsa: Sojoji sun sako shahararren jarumin Nollywood da suka damke

  • Rundunar soji ta sako jarumin masana'antar Nollywood da ta cafke ranar Alhamis bisa zargin alaƙa da ƙungiyar IPOB
  • Jarumar Nollywood, Chizzy Alichi, ta bayyana cewa Kawu Agu, ya dawo cikin koshin ƙafiya kuma babu wani abun damuwa
  • Jarumin dai ya faɗa cewa an kama shi ne a birnin Onitsha, jihar Anambra, lokacin da yake raba kayan abinci ga masu ƙaramin karfi

Abuja - Rundunar sojojin ƙasar nan ta sako shahararren jarumin masana'antar Nollywood, Chinwetalu Agu, wanda ta cafke ranar Alhamis da ta gabata.

Jami'an sojojin sun cafke mista Agu ne bisa zarginsa da tallafawa haramtacciyar ƙungiyar yan awaren IPOB.

Ɗaya daga cikin fitattun jarumai mata na masana'antar ta Nollywood, Chizzy Alichi, ita ce ta sanar da haka shafinta na dandalin sada zumunta Instagram.

Jarumi Chinwetalu Agu
Da Duminsa: Sojoji sun sako shahararren jarumin Nollywood da suka damke Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A wani hoton bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta, Jarumin yace sojojin sun kama shi ne a Birnin Onitsha, jihar Anambra, yayin da yake raba kayan abinci ga mabukata.

Kara karanta wannan

Tauraron Nollywood ya shiga hannun Sojoji, ana zarginsa da ba ‘Yan ta’adda goyon baya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar jarumin mutanen da yake raba wa kayan abincin na sanye ne da kayan dake ɗauke da hoton fitowar rana, ba wai kakin yan IPOB ba kamar yadda akai zargi.

Yaushe aka sako jarumin?

Jaruma Chizzy Alichi, lokacin da take bayyana halin da ake ciki game da kame Agu, tace jami'an sojiji sun sako shi.

A rubutun da ta yi, tace:

"An sako kawu Chinwetalu Agu, kuma yana cikin ƙoshin lafiya, babu wani abun damuwa. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah da kuma duk wanda ya bada gudummuwarsa ta kowane fanni."

Bamu ci mutuncinsa ba - Sojoji

A wani jawabi da kakakin rundunar sojojin ƙasar nan, Birgediya janar Onyema Nwachukwu, ya fitar ranar Alhamis, yace babu wani cin mutunci da aka yiwa Agu.

A wani labarin kuma An Kama Ɗan Shahararren Jarumi a Masana'antar Shirya Fina-Finan India

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Buƙaci a Kama Musulmin Da Suka Kashe Fasto a Kano

Rahotanni na nuni da cewa hukumomin tsaro sun cafke ɗan shahararren jarumin Bollywood, Shah Rukh Khan, wato Aryan Khan.

Khan ya shiga hannun jami'an hukumar NCB ne bisa zarginsa da shan miyagun kwayoyi a lokacin wata liyafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262