Yan bindiga sun kashe yan sanda, Lauyoyi tare da kona fasinjojin wata mota

Yan bindiga sun kashe yan sanda, Lauyoyi tare da kona fasinjojin wata mota

  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu tsagerun yan bindiga sun kashe jami'an yan sanda da wasu lauyoyi a Ebonyi
  • Lamarin ya faru ne a ƙauyukan Isu and Onicha Igboeze, dake ƙaramar hukumar Onicha a cikin jihar
  • Wannan na zuwa ne ƙasa da awanni 24 bayan gwamnan jihar Dave Umahi, ya yi barazanar kama iyayen yan bindiga

Ebonyi - Aƙalla mutun 10 sun rasa rayuwarsu, ciki harda jami'an yan sanda, yayin da miyagun yan bindiga suka kai hari ƙauyukan Isu da Onicha Igboeze, ƙaramar hukumar Onicha, jihar Ebonyi.

Maharan sun hallaka jami'an yan sanda biyu a Isu, yayin da aka kashe sauran a Onicha Igboeze, duk a ƙaramar hukuma ɗaya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Hakanan kuma rahoto ya tabbatar da cewa daga cikin waɗanda yan bindigan suka kashe harda lauyoyi guda biyu.

Kara karanta wannan

Bollywood: An Kama Ɗan Shahararren Jarumi a Masana'antar Shirya Fina-Finan India

Jihar Ebonyi
Yan bindiga sun kashe yan sanda, Lauyoyi tare da kona fasinjojin wata mota Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta gano cewa lamarin ya ritsa da lauyoyin ne yayin da hanya ta biyo da su inda yan bindigan suke.

The Nation ta rahoto cewa Bayan kashe lauyoyin, an gano cewa miyagun sun yi awon gaba da wata mota mallakin waɗanda suka kashe.

Maharan sun kona mota da mutanen ciki

Hakanan kuma a Onicha Igboeze, wasu miyagun sun ƙone fasinjoji bakwai a cikin motar da suke tafiya.

Wannan mummunan lamarin ya faru ne a kan hanyar Onicha Igboeze, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Loveth Odah, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Odah ya bayyana cewa tuni kwamishinan yan sandan jihar, Aliyu Garba, ya tura tawagar jami'ai na musamman zuwa yankin da lamarin ya shafa.

Kara karanta wannan

Hauka maganinta Allah: Wani mutumi ya hallaka matarsa mai kaunarsa da ɗan da suka haifa

Wannan mummunan lamarin ya faru ne awanni 24 kacal bayan gwamna Dave Umahi ya yi barazanar damƙe iyayen yaran dake tada zaune tsaye.

A wani labarin na daban kuma Miyagu 30 sun mutu yayin da mayakan Ansaru da Yan bindiga suka fafata da juna a Kaduna

Rahotanni daga Kaduna sun nuna cewa mayaƙan Ansaru sun hallaka yan bindiga aƙalla 30 a karamar hukumar Birnin Gwari.

Bangarorin biyu sun fara gwabzawa da junansu ne tun bayan sharaɗin da Ansaru ta kafa wa yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel