An tattauna da 'yan bindiga a Zamfara, sun sako mutane sama da 200
- Jihar Zamfara ta tabbatar da an sako wasu mutane sama da 200 da ke hannun 'yan bindiga
- A halin da ake ciki, ana kan jiran isowarsu zuwa Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara
- Wannan na zuwa ne jim kadan bayan rasuwar mahaifin kakakin majalisar jihar a hannun 'yan bindiga
Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara a ranar Alhamis ta ce ta tabbatar da sakin akalla mutane 200 da ‘yan bindiga suka sace ta hanyar tattaunawa ta lumana da sauran matakan tsaro.
Mukaddashin Gwamnan Zamfara, Nasiru Magarya, ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin Taron Shugabannin Majalisar Dokokin Jihohin Najeriya, a Gusau.
Mista Magarya, wanda shine kakakin majalisar dokokin Zamfara, ya tarbi tawagar, wacce ta kai masa ziyarar jaje bisa rasuwar mahaifinsa, Mu’azu Magarya, Daily Nigerian ta ruwaito.
Yanzu Yanzu: Na kai karar Malami gaban Buhari, kuma bai amince da dokar ta-baci ba a Anambra - Gwamna Obiano
A baya mun kawo muku rahoton cewa, Mahaifin mai kakakin majalisar ya mutu yayin da yake hannun 'yan bindiga.
Tawagar, a karkashin jagorancin Shugaban Taron kuma Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Abubakar Sulaiman, ta kuma kunshi shugabannin majalisar Kano, Katsina da Yobe.
Mista Magarya ya yabawa musu bisa ziyarar, ya kara da cewa kalubalen tsaro da ke damun Zamfara ya zama abin damuwa ga gwamnatin da Gwamna Bello Matawalle ke jagoranta.
Ya kuma, ya tabbatarwa da maziyarta da mutanen jihar kudirin gwamnati na magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Da yake magana kan jimamin da ya shiga kan rashin mahaifinsa, ya kuma yi godiya cewa:
“Alhamdulillah, an yi nasarar kubutar da iyalan ciki har da jaririn dan watanni uku.
“Amma abin takaici, ga mahaifin mu, Alhaji Mu’azu Magarya, lokacin sa ya zo kuma a matsayin mu na Musulmi, dukkan mu mun yi imani cewa dole ne kowane rai na da farko da karshe.
“A madadin danginmu, Gwamnatin Zamfara da Majalisar Dokoki ta Jiha, muna godiya da wannan ziyarar.
"Ina farin cikin sanar da ku cewa gwamnatin jihar ta tabbatar da sakin sama da mutane 200 da aka yi garkuwa da su ta hanyar zaman lafiya da tattaunawa, wanda gwamnatin yanzu karkashin jagorancin gwamnan jihar ta fara."
Mista Magarya ya lura cewa mutanen da aka saki suna kan hanyarsu ta zuwa Gusau, babban birnin jihar kuma za su iso kowane lokaci daga yanzu.
Tun da farko, Shugaban Taron Kakakin Majalisa Sulaiman, ya ce sun zo ziyarar ne domin jajantawa Kakakin Majalisar Zamfara, danginsa da mutanen jihar, kan rasuwar mahaifinsa.
Da zafi-zafi: Gwamnatin Neja ta ce za ta sa kafar wando daya da masu ba 'yan bindiga bayanai
A wani labarin, Gwamnatin jihar Neja ta sha alwashin tabbatar da kamawa tare da gurfanar da wadanda ke ba da bayanan sirri ga 'yan bindigar da ke addabar wasu sassan jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane, ya bayyana hakan a wani taron kwana 1 kan matsalar fashi da makami, wanda Cibiyar Binciken Tarihi da Takaddama ta Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida, Lapai, Jihar Neja ta shirya.
A cewar Matane:
“Barnar masu ba da bayanai da ke musayar bayanan sirri tare da 'yan bindigan kan yadda suke kai hare-hare sun kara dagula yanayin rashin tsaro a yanzu musamman a wasu sassan jihar.
Asali: Legit.ng