Da zafi-zafi: Gwamnatin Neja ta ce za ta sa kafar wando daya da masu ba 'yan bindiga bayanai

Da zafi-zafi: Gwamnatin Neja ta ce za ta sa kafar wando daya da masu ba 'yan bindiga bayanai

  • Gwamnatin Neja ta bayyana bukatar yaki da masu ba 'yan bindiga bayanan sirri na tsaro
  • Gwamnati ta ce, bayanan da 'yan bindiga ke samu daga mutanen shi ke kara ta'azzara rashin tsaro
  • Gwamnati ta bayyana wasu abubuwan da ta fahimta game da yawaitar kai hare-hare a yankunan

Neja - Gwamnatin jihar Neja ta sha alwashin tabbatar da kamawa tare da gurfanar da wadanda ke ba da bayanan sirri ga 'yan bindigar da ke addabar wasu sassan jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane, ya bayyana hakan a wani taron kwana 1 kan matsalar fashi da makami, wanda Cibiyar Binciken Tarihi da Takaddama ta Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida, Lapai, Jihar Neja ta shirya.

Gwamnatin jihar Neja za ta fara yaki da masu ba 'yan bindiga bayanan sirri
Taswirar jihar Neja | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A cewar Matane:

“Barnar masu ba da bayanai da ke musayar bayanan sirri tare da 'yan bindigan kan yadda suke kai hare-hare sun kara dagula yanayin rashin tsaro a yanzu musamman a wasu sassan jihar.

Kara karanta wannan

An tattauna da 'yan bindiga a Zamfara, sun sako mutane sama da 200

"Don haka, dole ne a tattara ayyukan tsaro na hadin gwiwa tare da dorewa don fatattakar 'yan bindigan, masu ba da bayanai da sauran masu aikata laifuka a jihar."

Ya kuma koka da yadda rikicin manoma da makiyaya ya kai ga rashin tsaro, tare da bayyana bukatar gwamnati ta magance, rigingimun kan iyaka, talauci, jahilci, rashin aikin yi da yaduwar kananan makamai da manya, da sauran su.

Matane ya jaddada bukatar hadin kai da dorewar ayyukan tsaro da sa ido kan yaduwar makamai, tabbatar bin diddigi, tsarin sadarwa da kafa rundunar 'yan sanda don kawo karshen ta'addanci.

Garin kai hari, 'yan sanda suka samu nasarar harbe shugaban 'yan bindiga a jihar Neja

Jami’an rundunar da ke yaki da garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan Najeriya, tare da tallafin 'yan banga, a ranar Litinin 30 ga watan Agusta sun hallaka wani sanannen shugaban ‘yan bindiga, Jauro Daji, a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Burodi ya zama nama: Tsadar burudo da 'Pure water' ya addabi babban birni Abuja

Sun kuma kashe wasu 'yan bindiga da yawa yara ga Daji a yankin Kontagora na jihar. An kuma kwato babura goma daga hannun 'yan bindigar, a ruwayar Punch.

A cewar majiyar, rundunar 'yan sandan ta yi aiki da sahihan bayanan sirri kuma ta yi wa 'yan bindigan kwanton bauna, inda suka kashe Daji, tare da yaransa, wadanda ke kokarin tsallaka wani rafi a cikin daji, don yin garkuwa da mutane a wani gari.

Rashin tsaro: 'Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a jihar Neja

Wani rahoton gidan talbijin na AIT ya kawo cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe sojoji biyu a wani hari da aka kai garin Kagara da fadar Sarkin, a jihar Neja.

Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a garin Minna, babbar birnin jihar, jim kadan bayan ya ziyarci sojoji goma sha biyu da suka jikkata wadanda ke karbar magani a asibitin Ibrahim Badamasi Babangida.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

Gwamnan ya kuma ce wasu daga cikin sojojin da suka jikkata suna samun kulawar likitoci a wani asibiti da ke Kaduna, sashin Hausa na BBC ya kuma ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel