Kano: Dalibar jami'ar Bayero ta tsero daga hannun masu garkuwa da mutane

Kano: Dalibar jami'ar Bayero ta tsero daga hannun masu garkuwa da mutane

  • Sakina Bello, dalibar aji uku a jami'ar Bayero da ke Kano wacce miyagu suka yi garkuwa da ita ta tsero daga hannun masu garkuwa da mutane
  • An tattaro cewa, ba a biya kudin fansa har miliyan dari da suka bukata ba, kuma ta ce kwatsam ta gan ta wuraren Sabon Gari
  • Kakakin rundunar 'yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce an mika ta asibiti ne bayan da ta kira yayanta ta sanar da shi inda ta ke

Kano - Dalibar jami'ar Bayero da ke Kano wacce masu garkuwa da mutane suka sace a tsakar birnin Kano mai suna Sakina Bello, ta tsero daga hannun miyagun da suka sace ta.

Idan za a tuna, dalibar aji ukun da ke karantar fannin ilimin tsirrai, an sace ta wurin karfe 3 na yammacin ranar Talata yayin da ta ke hanyar zuwa gida a Keke, LIB ta ruwaito.

Read also

Femi Adesina: Ya dace a ce Sanata Abaribe ya na can ya na shakawata a gidan fursuna

Kano: Dalibar jami'ar Bayero ta tsero daga hannun masu garkuwa da mutane
Kano: Dalibar jami'ar Bayero ta tsero daga hannun masu garkuwa da mutane. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

Daga bisani, wadanda suka yi garkuwa da ita sun kira 'yan uwan ta da safiyar Laraba tare da bukatar kudin fansa har miliyan dari, LIB ta wallafa.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, ba a biya kudin fansa ba kuma daga bisani da kan ta ta kira dan uwan ta inda ta sanar da shi ta tsero.

A yayin tabbatar da rahoton, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Kiyawa, ya ce dalibar ta yi ikirarin cewa ta tsero daga wadanda suka sace ta kuma ta samu kan ta a wuraren Sabon Gari.

Ya ce 'yan sanda sun dauke ta tare da kai ta asibiti, ya kara da cewa "ba bu abinda za su bari ba tare da sun bincika ba" domin gano yadda lamarin ya faru.

Read also

Kaduna: 'Yan sanda sun ceto mutum 6 da aka yi garkuwa da su

'Yan sandan Katsina sun damke dan Nijar mai shekaru 18 da ke kai wa 'yan bindiga man fetur

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta yi ram da wani matashi mai karancin shekaru da ake zargi da kai wa 'yan fashin dajin jihar man fetur.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, wanda ya bayyana hakan a wata takarda a Katsina ranar Laraba, 6 ga watan Oktoba, ya ce wanda ake zargin mai shekaru 18 a duniya sunansa Almustafa Kabir daga jamhuriyar Nijar.

Kabir kwarrare ne wurin samar da man fetur ga 'yan fashin dajin da suke dajikan jihar Katsina bayan gwamnati ta saka wasu matakan ganin bayansu, Kamar yadda LIB suka wallafa.

Source: Legit

Online view pixel