'Yan sandan Katsina sun damke dan Nijar mai shekaru 18 da ke kai wa 'yan binidiga man fetur

'Yan sandan Katsina sun damke dan Nijar mai shekaru 18 da ke kai wa 'yan binidiga man fetur

  • Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta cafke wani matashi mai shekaru sha takwas da laifin samarwa da 'yan fashin daji man fetur
  • Almustafa Kabir matashi ne dan asalin kauyen Dan'arua da ke jamhuriyar Nijar kuma an kama shi a titin Magama zuwa Jibia ta Katsina
  • Ya na dauke da ledoji cike da fetur yayin da sojoji suka gan shi tare da tare shi kuma ya amsa cewa 'yan bindiga zai kai wa

Katsina - Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta yi ram da wani matashi mai karancin shekaru da ake zargi da kai wa 'yan fashin dajin jihar man fetur.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah, wanda ya bayyana hakan a wata takarda a Katsina ranar Laraba, 6 ga watan Oktoba, ya ce wanda ake zargin mai shekaru 18 a duniya sunansa Almustafa Kabir daga jamhuriyar Nijar.

Read also

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

'Yan sandan Katsina sun damke dan Nijar mai shekaru 18 da ke kai wa 'yan binidiga man fetur
'Yan sandan Katsina sun damke dan Nijar mai shekaru 18 da ke kai wa 'yan binidiga man fetur. Hoto daga lindaikejisblog.com
Source: UGC

Kabir kwarrare ne wurin samar da man fetur ga 'yan fashin dajin da suke dajikan jihar Katsina bayan gwamnati ta saka wasu matakan ganin bayansu, Kamar yadda LIB suka wallafa.

"A ranar 5 ga watan Oktoban nan da muke ciki wurin karfe 1 na rana, rundunar ta yi nasarar damke Almustafa Kabir mai shekaru goma sha takwas a duniya na kauyen Dan'arau da ke jamhuriyar Nijar sakamakon kwarewa da yayi wurin kai wa 'yan fashin daji man fetur," Gambo yace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Dakarun sojin da ke sintiri kan titin Magama zuwa Jibia ne yayin da suka kama shi dauke da fetur a cikin ledoji. A yayin bincike, ya bayyana cewa ya aikata laifin kuma ana cigaba da bincike a halin yanzu."

Ta'addanci: Gwamnonin yankin tafkin Chadi takwas sun gana a Kamaru

A wani labari na daban, Gwamnoni takwas na yankin tafkin Chadi sun gana a birnin Yaounde da ke jamhuriyar Kamaru a ranar Litinin inda suka tattauna kan matsalar tsaro da kuma hadin kan yankin, Daily Trust ta wallafa.

Read also

Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace dalibar BUK a Kano

Taron da hukumar kula da tafkin Chadi, tare da hadin guiwar African Union, shirin cigaban majalisar dinkin duniya suka hada, gwamnatin Kamaru tare da hadin guiwar kungiyar gwamnonin tafkin Chadi suka bada masauki.

Gwamnoni shida da suka hada da Babagana Umara Zulum na jihar Borno, Issa Lamine na Diffa daga Nijar, Midjiyawa Bakari na arewacin Kamaru, Abate Edii Jean na yankin arewacin Kamaru, Mahamat Fadoul Mackaye na yankin Lac da ke Chadi da Amina Kodjyana Agnes Hadjer ta Chadi duk sun halarci taron yayin da gwamnonin jihohin Adamawa da Yobe suka tura wakilai.

Source: Legit

Online view pixel