Sabbin hotunan jaruma Maryam Yahaya yayin da take kara murmurewa

Sabbin hotunan jaruma Maryam Yahaya yayin da take kara murmurewa

  • Wasu sabbin hotunan jaruma Maryam Yahaya sun bayyana yayin da take ci gaba da murmurewa
  • A cikin hotunan, an gano jarumar cikin shiga ta kamala, sai dai tayi rama sosai wanda ke nuna tayi jinya sosai
  • Mabiya shafukan soshiyal midiya sun yi martani inda wasu suka shawarce ta da ta daina hotuna saboda baki

Sabbin hotunan shahararriyar jarumar Kannywood wacce ke fama da matsanaciyar rashin lafiya, Maryam Yahaya sun bayyana yayin da take kara murmurewa.

Kamar yadda aka yi hira da ita a kwanakin baya bayan cece-kuce da aka dunga yi game da cutar da ke damunta, Maryam ta fito ta bayyana cewa cutar Typoid da Malaria ne ke damunta.

Sabbin hotunan jaruma Maryam Yahaya yayin da take kara murmurewa
Sabbin hotunan jaruma Maryam Yahaya yayin da take kara murmurewa Hoto: real_maryamyahaya/_garkuwanarewa
Asali: Instagram

Sai dai duk da haka, wasu da dama na kokwanto kan cutar da tace tana damunta duba ga yadda ta rame da sauyawar kamanninta.

Kara karanta wannan

Burodi ya zama nama: Tsadar burudo da 'Pure water' ya addabi babban birni Abuja

A cikin sabbin hotunan da shafin instagram na _garkuwanarewa ta wallafa nata, an gano jarumar cikin shiga ta kamala da lullubi a kafadarta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai akwai rama sosai a tattare da ita wanda ke nuna cutar tayi mata mummunan kamu, amma ga dukkan alamu sauki na samuwa a gareta.

Shafin ya wallafa hottunan da rubutu kamar haka:

"HASBUNALLAH
"Sabbin hotunan Jarumar Kannywood Maryam Yahaya wadda take fama da cutar Typoid da Malaria a cewarta.
"Jama'a wannan fa shine ma'anar duniya ta maka wa'azi idan ka ki jin wa'azin Malamai, da sauran mutanen kirki ka biyewa rudin shaidan da na 'yan duniya.
"An cutar da Maryam Yahaya, kuma wadanda sukayi sanadin cutar da ita din sun gujeta a halin da take ciki tana bukatar taimakonsu, wannan bincike ne da na gudanar tun da jimawa akan rashin lafiyar ta.

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Gwamnatin Neja ta ce za ta sa kafar wando daya da masu ba 'yan bindiga bayanai

"Allah Ka saka mata, Ka sa hakan ya zama kaffara a gareta."

Ga wasu daga cikin martanin jama'a:

bilkisu6312 ta ce:

"To Shin dolene saita yada Hotunan ta wai"

cutee_janah ta rubuta:

"Ta kuwa sha qunshinta abunta"

_rqpson ya ce:

"Allah ya bata lpy "

itz_meriem_ ta rubuta

"ALLAH ya bata lafiya "

Tauraruwar Kannywood Maryam Yahaya Ta Bayyana Cutar Dake Damunta Yasa Aka Ji Ta Shiru

A baya mun kawo cewa, daya daga cikin fitattun jarumai mata dake tashe a masana'antar shirya fina-fanai Kannywood, Maryam Yahaya, tace cutar taifod da Maleriya ke damunta.

Jarumar ta faɗi hakane yayin wata fira da tayi da BBC Hausa, tace wannan dalilin ne yasa aka daina ganinta a cikin sabbin fina-finan Hausa.

Maryam Yahaya ta kuma yi watsi da wata jita-jita da mutane ke yaɗawa a kanta cewa tana fama da cutar iska wato jifan aljanu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel