Buhari ya yi alkawari Gwamnatinsa za ta kammala manyan ayyukan da aka fara kafin ya bar mulki

Buhari ya yi alkawari Gwamnatinsa za ta kammala manyan ayyukan da aka fara kafin ya bar mulki

  • Muhammadu Buhari ya bayyana irin kokarin da gwamnatinsa ke yi a Najeriya
  • Shugaban kasar yace Gwamnatin Tarayya za ta kaddamar da ayyukanta a 2023
  • Ana sa ran a kaddamar da duk wasu tituna da hanyoyin jiragen kasan da ake yi

Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashi gwamnatinsa za ta kammala duka wasu muhimman ayyuka da take yi a jihohin kasar nan.

Jaridar Leadership ta rahoto Mai girma Muhammadu Buhari yana cewa zai karasa ayyukan tituna, wuta, aikin noma da sauran kwangilolin da ya bada.

Buhari ya yi alkawari kafin ya bar kan gadon gwamnati, zai kaddamar da duk wasu ayyuka da ake yi a bangaren kiwon lafiya da ilmi da titunan jirgin kasa.

Kara karanta wannan

Za ka iya karban bashi don aiwatar da Kasafin Kudin 2022, Shugaban Majalisa ga Buhari

Rahoton yace shugaban Najeriyan ya bada wannan tabbaci a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa a gaban ‘yan majalisar tarayya dazu.

Shugaban kasar yake cewa duk da matsalar rashin kudin shiga, gwamnatin tarayya ta na biyan bashin da ke kanta, kuma ta biya duk wasu albashin ma’ikata.

Buhari
Buhari ya gabatar da kasafin kudi Hoto: www.naijanews.com
Asali: UGC

Abin da Buhari ya fada wa 'Yan majalisa

“Mun yi nisa a ayyukan titunan jirgin kasa da za su hada bangarorin kasar nan. Ina farin cikin fadar an gama dogon Legas zuwa Ibadan, kuma ya fara aiki.”
“Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna yana aiki sumul. An kammala aikin dogon Itakpe zuwa Ajaokuta, an kaddamar bayan sama da shekaru 30 da fara aikin.”
“Ana kokarin gama jirgin Ibadan zuwa Kano. Za a soma titin Fatakwal zuwa Maiduguri da Kalaba zuwa Legas kwanan nan, wanda za su hada Kudu da Arewa."

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 10 da Shugaba Buhari ya fada a jawabinsa ga yan majalisa ranar Alhamis

“Muna sa ran mu kaddamar da mafi yawan ayyukan nan kafin karshen wa’adinmu a 2023.” - Buhari

A jawabinsa, Buhari yace an yi nisa a ayyukan wuta da nufin a rika samun lantarki sosai nan da 2025. Sannan ya ambaci aikin titunan da ake ta bazawa a jihohi.

A ranar Alhamis, 7 ga watan Oktoba, 2021 ne Buhari ya gabatar da kasafin kudin da ya rada wa suna da ‘Budget of Economic Growth and Sustainability’ a majalisa.

Makarkashiya a zaben 2023?

A yau ne kuma aka ji CUPP tace akwai makarkashiya a game da zaben 2023. Kakakin kungiyar, Ikenga Ugochinyere yace watakila a ki aiki da na’urar zamani a zaben.

Ugochinyere yace ana so ayi ta jan maganar yi wa dokar zaben kwaskwarima har 2022. A cewarsa har ana ba ‘Yan Majalisa cin hanci domin cin ma wannan manufa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel