Likitoci sun yi sa'a ni ne a matsayin minista, Ministan Buhari ya koɗa kansa

Likitoci sun yi sa'a ni ne a matsayin minista, Ministan Buhari ya koɗa kansa

  • Ministan kwadugo da samar da aikin yi, Dakta Chris Ngige, yace likitoci masu neman kwarewa sun taki sa'a kasancewarsa a matsayin minista
  • Ngige ya bayyana cewa shi cikakken likita ne, don haka lokacin da lamarinsu ya taso ya fahimci komai cikin kankanin lokaci
  • Ministan ya kuma nuna rashin jin daɗinsa bisa saka siyasa a lamarin da masu jagorantar NARD na baya suka yi

Abuja - Dakta Chris Ngige, ya shaidawa likitoci masu neman kwarewa cewa sun taki sa'a da ya kasance shi ne a kujerar ministan kwadugo da samar da ayyukan yi.

Punch ta rahoto ministan na tabbatar wa likitocin cewa gwamnati ta cimma matsaya wajen cika musu bukatunsu yayin taron ta da ƙungiyar likitoci (NMA) da kuma shugabannin NARD.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Buƙaci a Kama Musulmin Da Suka Kashe Fasto a Kano

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rahoto cewa taron tsakanin FG da kungiyoyin NMA da NARD ya gudana ne ranar Laraba a Abuja.

Ministan kwadugo, Dakta Chris Ngige.
Likitoci sun yi sa'a ni ne a matsayin minista, Ministan Buhari ya koɗa kansa Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ngige yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kun taki sa'a da kuka same ni, cikakken likita, a nan ma'aikatar kwadugo. Lokacin da lamarin bukatunku ya taso, nan da nan na fahimci komai."

Meya jawo dogon lokaci likitocin na yajin aiki?

Hakanan kuma ministan ya nuna rashin jin daɗinsa da shugabannin ƙungiyar NARD da suka gabata bisa rashin sanar da mambobinsu halin da ake ciki game da tattaunawa da FG.

A cewarsa, wannan shine babban maƙasudin da yasa yajin aikin ya ɗauki dogon lokaci ba tare da cimma matsaya ba.

"Shugabannin NARD da suka gabata basu sanar da mambobinsu halin da ake ciki, banda haka da abun bai kai yanzu ba."
"Mun sani cewa muna da yan adawa, amma hakan ba yana nufin ba za'a yaba mana ba idan mun yi abinda ya kamata."

Kara karanta wannan

Rikicin VAT: Babu abun da Arewa za ta rasa, in ji jigon APC

"Inda shugabannin NARD da suka gabata basu saka siyasa a ciki ba, kamata ya yi su rinka kai rahoto ga mambobinsu, musamman lokacin da manyan likitoci suka shigo cikin.maganar."

A wani labarin na daban kuma kun ji cewa ƙungiyar likitoci NARD ta bayyana dalilan da yasa ta janye yajin aikin da ta shafe watanni tana fafatawa

Yajin aikin NARD, wanda ya shafe sama da watanni biyu ya jefa asibitocin gwamnati da kuma marasa lafiya cikin mummunann yana yi.

Sabon shugaban NARD, Godiya Ishaya, wanda ya tabbatar da janye yajin aikin, yace sun ɗauki matakin ne bayan taron kwamitin zartarwa na ƙungiyar ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel