Dalilin da ya sa ƴan bindiga su ke kai farmaki wasu garuruwa 2 a Katsina, Ƴan Sanda

Dalilin da ya sa ƴan bindiga su ke kai farmaki wasu garuruwa 2 a Katsina, Ƴan Sanda

  • Bincike ya bayyana dalilin da ya sa ‘yan bindiga su ka addabi garuruwa 2 a Katsina
  • An gano cewa farmakin ya biyo bayan halaka fulani da wasu ‘yan sa kai suke yi ne
  • Ko ranar Talatar da ta gabata sai da ‘yan bindiga su ka halaka mutane 10 a Batsari

Jihar Katsina - ‘Yan sanda sun gano cewa dalilan da ya sa ‘yan bindiga su ke ta halaka mutane a jihar ya biyo bayan hakala Fulani da wasu kungiyoyin ‘yan sa kai su ke ta yi ne.

Premium Times ta ruwaito yadda ‘yan bindigan su ka halaka mutane 10 a garin Yasore da ke Batsari a daren Talata.

Dalilin da ya sa ƴan bindiga su ke kai farmaki wasu garuruwa 2 a Katsina, Ƴan Sanda
Taswirar Jihar Katsina. Hoto: Premium Times
Source: Twitter

Read also

Kada ka damu kan ka, ƴan Najeriya ba su cancanci taimako ba, Jaruma Ruth Kadiri

Jama’an garin da dama sun samu raunuka da dama sannan ‘yan bindigan sun kone musu gidajen su da shaguna.

Yayin tattaunawa da manema labarai a Katsina, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isa ya ce ‘yan bindigan su na mayar da martani ne.

A cewar sa ‘Yan sa kai ne suka ja wa mutanen garin

A cewar sa, farmakin da aka kai Yasore, ‘yan bindigan sun shiga har cikin kauyen da baburan su, sannan sun yi amfani da miyagun makamai wurin kai wa jama’a farmaki.

Kamar yadda ya bayyana bisa ruwayar Premium Times:

“Binciken mu ya nuna mana cewa ‘yan bindiga suna kawo harin ne a matsayin martanin halaka Fulani da wasu ‘yan sa kai su ka dinga yi. Wadannan ‘yan sa kan sun yi ta halaka Fulanin ba tare da sun aikata wani laifi ba.”

Baya ga Yasore, Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce su na ta bincike akan halaka jama’a da ake ta yi a Daudawa dake karamar hukumar Faskari.

Read also

Zamfara: Ƴan bindiga sun kashe mutum 19, ciki har da ƙananun yara, sun ƙone shaguna da gidaje

Kamar yadda ya bayyana:

“Ko a Daudawa akwai batun mayar da martani na halaka mutanen da ba su ji ba basu gani ba da ‘yan sa kai su ka yi. Amma tun makon da ya gabata muke ta bincike akan lamarin. Wasu matasan ‘yan sa kai su na ta daukar doka a hannun su. Mun tattaro bayanai akan ta’addanci a kananun hukumomi kamar Bakori, Funtua, Batsari da sauran su akan halaka ‘yan Fulani.”

Karamar hukumar Faskari da Batsari ma su na cikin kananun hukumomin da suke fama da ta’addanci.

An katse duk wasu hanyoyin sadarwa da kuma kasuwannin mako a yankunan don kawo karshen ta’addanci.

'Yan bindiga sun kashe mutum 10, sun raunata wasu da dama a sabon harin da suka kai Katsina

Tun a baya, kun ji cewa 'yan bindiga a safiyar ranar Talata sun kashe mutum 10 sun kuma raunata wasu da dama yayin sabon harin da suka kai inda suka kona shaguna da gidaje a Yasore, jihar Katsina, mazauna garin suka shaidawa Premium Times.

Read also

Miyagun yan bindiga sun bude wa masallata wuta, Sun kashe aƙalla 10 a jihar Katsina

Yasore ba shi da nisa da Batsari, hedkwatar karamar hukumar Batsari.

Batsari na daya daga cikin kananan hukumomin da 'yan bindiga ke yawan kai hari. Yana da iyaka da dajin Rugu, karamar hukumar Katsina da Zurmi a jihar Zamfara.

Source: Legit

Online view pixel