Kada ka damu kan ka, ƴan Najeriya ba su cancanci taimako ba, Jaruma Ruth Kadiri
- Jarumar fina-finai, Ruth Kadiri ta yi wata wallafa wacce ta janyo cece-kuce a shafin ta na Instagram
- Kamar yadda ta ce kada wani ya damu kan sa akan ‘yan Najeriya don ba su cancanci taimako ba
- Kamar yadda ta bayyana, ‘yan Najeriya da dama su na fatan ganin rayuwar wani sananne ta tagayyara
Jarumar fina-finan Nollywood, Ruth Kadiri ta bayyana ra’ayin ta dangane da halayyar ‘yan Najeriya.
Jarumar ta wallafa a shafin ta na kafar sada zumuntar zamani ta Instagram inda ta ce halayen ‘yan Najeriya su na nuna ba su cancanci taimako ba.
A cewar ta ‘yan Najeriya da dama su na farin cikin karanta labarai akan yadda auren wasu sanannu ya wargaje.
A cewar ta ‘yan Najeriya ba su da burin da ya wuce ganin bayan wani sananne
Har ila yau, ta ce ba su da wani buri kamar su ji wata jaruma tana lalata da wani mutum mai aure.
Ta karashe wallafar ta ta inda take cewa gaskiya ‘yan Najeriya ba su cancanci a taiamaka mu su ba.
Kamar yadda jarumar ta yi wallafar, ta bayyan cewa:
“Me zai sa ka yi fada akan mutanen da ba sa son ka yi fada akan su?
“Me zai sa ka jajirce akan mutanen da idan ka yi wata wallafar nema mu su hakki a kafar sada zumunta za su bukaci ka yi shiru da bakin ka?
“Abinda kawai suke jira shi ne su ji yadda auren wani sananne ya lalace da kuma yadda wata sananna ta lalace da wani mutum mai aure.
“Kana kokarin kalubalantar wani dan siyasa, wasu mutane 10 masu maita, yunwa da neman gindin zama zasu zaburo su fara yakar ka.
“Yan Najeriya ba su cancanci wani taimako ba, kada ka damu kan ka.”
Take anan mutane da dama su ka fara cece-kuce a karkashin wallafar.
Dole ciki ya sa ki saduda da rayuwa, hotunan yadda juna biyu ya sauya wa wasu mata hallita
A wani labarin daban, mata da dama su na fuskantar canji a jikin su yayin da suke dauke da juna biyu, wasu su na yin haske yayin da wasu suke yin duhu kwarai. Akwai wadanda suke yin kiba sosai wasu kuma su rame.
Akwai matan da suke yin kyau ko a fuska yayin da wasu kuma kureje suke bayyana musu duk su canja.
Ba rashin gyara ne yake kawo hakan ba, ba kuma talauci ko kuncin rayuwa ba, hakanan ciki yake mayar da mata kuma abin a hankali ne yake faruwa.
Asali: Legit.ng