Wanda ya dace APC ta tsayar ya gaji shugaba Buhari a zaɓen 2023, Tsohon Minista ya magantu

Wanda ya dace APC ta tsayar ya gaji shugaba Buhari a zaɓen 2023, Tsohon Minista ya magantu

  • Tsohon minista a Najeriya, Adeseye Ogunlewe, ya bayyana cewa jigon APC, Bola Tinubu, shi ne ya fi cancanta ya gaji shugaba Buhari a 2023
  • Ogunlewe ya bayyana cewa a ranar Alhamis mai zuwa za'a ƙaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu reshen mahaifarsa, jihar Legas
  • Yace a halin yanzun babu wanda yafi Tinubu dace wa ya nemi takarar shugaban ƙasa a ƙarkashin APC

Lagos - Tsohon ministan ayyuka, Adeseye Ogunlewe, ya yi kira ga jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya gaggauta bayyana sha'awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023.

The cable ta ruwaito cewa tsohon ministan na ganin babu wanda ya dace APC ta tsayar ya gaji shugaba Buhari a 2023 kamar Tinubu.

Da yake jawabi a shirin gidan talabijin na Arise TV, ranar Talata, Ogunlewe, ya bayyana cewa Tinubu shine wanda ya cancanta ya gaji shugaba Buhari.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya yi magana kan yankin da ya kamata PDP ta kai takarar shugaban kasa a 2023

Shugaba Buhari da Bola Tinubu
Wanda ya dace APC ta tsayar ya gaji shugaba Buhari a zaɓen 2023, Tsohon Minista ya magantu Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Zamu fara yaƙin neman zaɓen Tinubu - Igunlewe

Ya ƙara da cewa, a ranar Alhamis mai zuwa zasu kaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu domin nuna goyon baya ga takararsa a zaɓen 2023.

Yace:

"Muna bukatar mutum mai zurfin tunani kuma mutum wanda ya sadaukar da kansa domin cigaban demokaraɗiyya. Saboda haka muna kira ga Sanata Tinubu ya fito ya bayyana."
"Ba abune mai sauki ba, sai an yi faɗi tashi, kuma sai ya jawo hankalin mutane kan cewa a shirye yake ya musu aiki."
"Ranar Alhamis zamu kaddamar da tawagar yaƙin neman zaɓensa a reshen jihar Legas domin haka zai nuna wa kowa kudirinsa na neman tikitin takara."

Shin dagaske Bola Tinubu ba shi da lafiya?

Tsohon ministan ya ƙara da cewa bayan kaddamarwa a Lagos, daga nan za'a matsa zuwa gangamin taron jam'iyya na ƙasa, inda anan za'a zaɓi wannan zai fafata takara karkashin APC.

Kara karanta wannan

Hauka maganinta Allah: Wani mutumi ya hallaka matarsa mai kaunarsa da ɗan da suka haifa

Ogunlewe ya ƙara da cewa:

"Ba shi da lafiya amma yana samun sauki sosai, yana da isasshen lokacin murmurewa kuma ya dawo ya faɗa mana zai tsaya takara ko a'a."
"Amma wajibi ya amimce, domin muna tunanin babu wanda ya dace ya jagoranci Najeriya sama da shi."

A wani labarin kuma kun ji cewa tuni magoya baya suka fara yaɗa fastocin Bola Tinubu a lungu da sako a jihar Legas

Duk da cewa babban jigon jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, bai bayyana niyyar shiga takara ba, wasu na ta yi masa yakin zabe.

Rahotanni sun ce an ga fastocin tsohon gwamnan na jihar Legas a wasu unguwannin Legas kamar su Ojota, Maryland, Ketu Ikeja, da kuma Lagos Island.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262