'Yan kasuwa a Kawo ta Kaduna sun yi watsi da umarnin El-Rufai sun koma harkokinsu

'Yan kasuwa a Kawo ta Kaduna sun yi watsi da umarnin El-Rufai sun koma harkokinsu

  • 'Yan kasuwa masu cin kasuwar mako-mako a kasuwar Kawo ta jihar Kaduna sun bijiriewa gwamnatin jihar
  • Wasu daga ciki sun fito domin ci gaba da kasuwancin da suka saba na mako-mako a cikin kasuwar
  • Wasu daga cikin 'yan kasuwar sun bayyana dalilin da yasa suka yanke shawarar komawa kasuwar

Kaduna- ‘Yan kasuwa a Kawo, sun bijirewa umarnin gwamna ta hanyar ci gaba da harkokinsu makonni uku bayan dakatar da kasuwannin mako-mako a wasu kananan hukumomi, ciki har da Kawo a karamar Hukumar Kaduna ta Arewa.

Daily Trust ta rahoto cewa kasuwar mako-mako na Kawo tana ci a ranar Talata lokacin da aka ziyarce ta, inda ‘yan kasuwa suka ce ba su da wani zabi illa su bijirewa gwamnati tunda ba a ba su wani madadi ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

'Yan kasuwa a Kawo ta jihar Kaduna sun yi watsi da umarnin El-Rufai sun koma harkokinsu
Gefen Kasuwar Kawo | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Duk da cewa ba a samu fitowar jama'a sosai ba, Abdulaziz Muhammad, wanda ke sayar da hatsi ya ce bai damu ba saboda karin mutane da kwastomomi za su zo daga baya da rana.

A cewarsa:

"Wannan ita ce kasuwa ta mako-mako kawai a kusa da babban birni inda za mu iya siyar da kayanmu da yawa saboda ba a samun riba mai yawa a cikin sauran kwanakin sati.
“Idan ban fito na sayar da abin da nake da shi don ciyar da iyalina ba, gwamnati ba za ta ciyar da ni ba; ba za su ba ni kudi don kula da iyalina ba.
"Akwai bukatar gwamnati ta samar mana da wata hanya. Wannan ita ce sana’ar da na sani kuma na dogara da ita kuma ba ni da wani waje da zan je sai kasuwar Kawo.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari zai sake ciyo sabon bashin N6.258tr, Ministar Kudi

A nasa bangaren, Ibrahim Abdullahi, mai sayar da tumatir daga Maraban Jos, ya ce ya bijirewa gargadin abokai da dangi ta hanyar zuwa kasuwa saboda ba shi da zabi.

Idan baku manta ba, mun kawo muku rahoto da muka samo daga Samuel Aruwan cewa, gwamnatin jihar Kaduna ta katse hanyoyin sadarwa a wasu sassan jihar tare da hana cin kasuwannin mako-mako a wasu sassan.

Wannan na zuwa ne yayin da lamurran tsaro suka ta'azzara a yankunan Arewa maso yamma, inda 'yan bindiga suka addabi jama'a.

Ba jihar Kaduna kadai ba, an samu jihohin Katsina da Zamfara da suka dauki irin wannan mataki don rage karfi da ayyukan 'yan ta'adda a yankunan.

Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara

A wani labarin daban, alamu sun bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da samun kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Zamfara duk da katse hanyoyin sadarwa a jihar.

Kara karanta wannan

Jerin kwamishinoni 11 da gwamnan Edo ya rantsar bayan watannin mulki ba kwamishinoni

Yayin da katsewar da kokarin sojoji ya rage barnar 'yan bindiga tare da kashe su, wasu mazauna jihar sun shaida wa BBC Hausa cewa an ci gaba da kai hare-hare da sace-sacen a jihar.

Don haka, duk da rokon da suke yi wa gwamnatin jihar na tsagaita wuta, kamar yadda Gwamna Bello Matawalle ya bayyana a ranar 10 ga Satumba, 'yan bindigan sun ci gaba da kai hari kan mazauna jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.