Shugaba Buhari zai sake ciyo sabon bashin N6.258tr, Ministar Kudi

Shugaba Buhari zai sake ciyo sabon bashin N6.258tr, Ministar Kudi

  • Buhari zai sake ciyo wasu sabbin basussuka don amfani a shekarar 2022
  • Ministar Kudi ta bayyana cewa gwamnatin Buhari ba zata daina ciyo basussuka ba
  • Ministar Kudin Buhari ta bayyana hakan ga manema labarai

Abuja - Ministar Kudi, Kasafin Kudi da shirye-shiryen kasa, Hajiya Zainab Ahmed Shamsuna, ta bayyana cewa majalisar zartaswar ta amince da kasafin kudin N16.39tr na 2022.

Hajiya Zainab ta bayyana hakan bayan taron majalisar zartaswar ranar Laraba yayin hira da manema labarai, rahoton DailyTrust.

Ta bayyana cewa gwamnatin Buhari zata karbi sabon bashi domin cimma burukan da aka shiryawa 2022.

Ta bayyana cewa a daina maganganu saboda basussukan da gwamnatin ke karba saboda ba su kadai bane wadanda suka fara karban basussuka.

A cewarta:

"Gwamnatoci sun dade suna karban basussuka kafin gwamnatin nan kuma za'a cigaba da karba saboda akwai muhimmanci mu karbi basussuka domin yin manyan ayyukan cigaba irinsu tituna, layukan dogo, gadoji, wutan lantarki, da kuma ruwan sha."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Manyan PDP sun amince dan arewa ya shugabanci jam'iyyar

"Idan muka dogara da kudaden shigan da muke samu, duk da cewa kudaden sun karu, albashi da wasu hada-hadan da gwamnati keyi na yau da kullum zasu kwashe kudaden shigan."
"Saboda haka muna bukatar karban bashi domin manyan ayyuka domin tabbatar da cewa muna kawo cigaba."

Abubuwan da kasafin kudin zai dogara kai

Ta bayyana wasu abubuwan da Buhari ya fadawa yan majalisa idan ya bayyana gabansu yau.

A cewarta abubuwan zasu dogara kan

1. Farashin danyan mai – $57 ga ganga

2. Za'a rika hakan gangan danyan mai milyan 1.88 kulli yaumin

3. Farashin Dala - N410.15/US$;

4. Kudin shiga na mai N3.15 trillion

5. Kudin shiga na haraji – N2.13 trillion.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng