Jerin kwamishinoni 11 da gwamnan Edo ya rantsar bayan watannin mulki ba kwamishinoni

Jerin kwamishinoni 11 da gwamnan Edo ya rantsar bayan watannin mulki ba kwamishinoni

  • Gwamnan jihar Edo ya yi sabbin nade-nade, ya kuma rantsar dasu a yau din nan Laraba
  • Ya bayyana cewa, ya kirkiri hanyar da zai gano masu kwazo da malalata a cikinsu don gyara
  • A baya gwamnan ya yi waje da dukkan kwamishinoninsa sannan ya nada sabbi saboda wasu dalilai

Jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki ya kaddamar da kwamishinoni 11 da masu ba shi shawara na musamman guda biyu a ranar Laraba 6 ga watan Oktoba a Benin a matsayin wadanda za su yi aiki a majalisar zartarwa ta jihar Edo.

Gwamnan ya umarci sabbin nade-naden da su tabbatar da aiki da gaskiya da rikon amana a cikin duk abin da za su yi a tsarin doka.

Da dumi-dumi: Gwamna Obaseki ya rantsar da kwamishinoninsa
Gwamna jihar Edo, Godwin Obaseki | Hoto: thenationonlineng.com
Asali: UGC

Ya gaya musu cewa an kirkiri katin bin diddigin kwazon aiki ga kowace ma'aikata don dora al'adun aiki da ke da inganci.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Manyan PDP sun amince dan arewa ya shugabanci jam'iyyar

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Katin zai bi diddigin muhimman ayyukan da ake aiwatarwa da isar da kowace ma’aikatar kuma za a nemi bahasin kwazo a kwata-kwata na shekara.
“Za a gudanar da kimantawa na yadda ake aiwatar da ayyuka da sakamakon da kowace ma’aikatar ta samu.
“Wadannan za su zama tushen karin bita da alaka da sauran mahimman hanyoyin aikin dan adam."

Ya bayyana bukatar kwamishinonin da suka jajirce su zama masu aiki don jiharsu da kuma ganin sun ciyar da jihar gaba.

Jerin kwamishinonin

Legit.ng Hausa ta tattaro daga majiyoyi masu tushe cewa, sabbin kwamishinonin da ya rantsar sune kamar haka:

  1. Mr Oluwole Iyamu
  2. Mrs Obehi Akoria
  3. Dr Joan Osa-Oviawe
  4. Osaze Uzamere
  5. Monday Osaigbovo
  6. Marie Edeko
  7. Joseph Eboigbe
  8. Musa Agbukor
  9. Isoken Omo
  10. Andrew Emwanta
  11. Mrs Otse Momoh-Omorogbe

Jerin masu bashi shawarwari a fannoni daban-daban

Kara karanta wannan

Likitoci sun yi sa'a ni ne a matsayin minista, Ministan Buhari ya koɗa kansa

Masu ba da shawara na musamman guda biyu da ya nada su ne

1. Crusoe Osagie

Gwamnan ya nada Osagie a matsayin mai ba da shawara na musamman, Ayyukan yada labarai

2. Sarah Esangbedo Ajose-Adeogun

Ita kuwa ita ce mai ba da shawara ta musamman, Dabaru, Manufofi, Ayyuka da Gudanar da Ayyuka.

Gwamnan PDP ya yi kusan shekara yana mulki shi kadai, babu Kwamishinoni a Gwamnati

A baya kadan, jaridar Daily Trust tace watanni goma kenan da Godwin Obaseki ya koma kujerar gwamna a jihar Edo, amma har yanzu bai nada kwamishinoni ba.

A ranar Talata, 28 ga watan Satumba, 2021, aka samu labari cewa gwamna Godwin Obaseki, ya aika wa majalisar dokoki jerin sunayen kwamishinoninsa.

Takardar da gwamnan ya aika wa majalisa tana kunshe da sunayen mutane 11 da ake so a ba kujerar kwamishina, da kuma masu bada shawarwari biyu.

Kamar yadda gwamnan ya bayyana ta hannun sakataren gwamnatin jihar, hadiman da aka zaba su ne; Crusoe Osagie da Sarah Esangbedo Ajose-Adeogun.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.