Burtaniya ta aiko sojojin ruwanta zuwa Najeriya don magance matsalar tsaro

Burtaniya ta aiko sojojin ruwanta zuwa Najeriya don magance matsalar tsaro

  • Burtaniya za ta turo sojojinta kan iyakokin ruwan kasashen Afrika a wani yunkuri na magance matsalar tsaro
  • Najeriya na daga cikin kasashen da za su mori wannan ziyara ta sojojin ruwa Burtaniya nan gaba kadan
  • Yankuna daban-daban a kasashen Afrika ta yamma na fuskantar matsalolin rashin tsaro daban-daban

Jirgin ruwan sintiri na Royal Navy mai suna HMS Trent, yana shirin tafiya zuwa tekun Guinea a wata manufa ta tallafawa abokan kawance a yankin Yammacin Afirka, inji rahoton Daily Trust.

A rahoton da Legit.ng Hausa ta tattaro daga Vanguard an kawo cewa, watannin da suka gabata rundunonin sojojin ruwa ciki har da Amurka da Burtaniya sun shiga atisayen tsaro na teku a yankunan Afrika.

Burtaniya ta aiko sojojin ruwanta zuwa Najeriya don magance matsalar tsaro
Sojojin Ruwa na Masarautar Burtaniya | Hoto: cloudinary.com
Source: UGC

Wata sanarwa dauke da sa hannun Ndidiamaka Eze, Jami'in Hulda da Jama'a na Ofishin Jakadancin Kasashen Duniya da Ci gaban Babbar Hukumar Burtaniya, a Najeriya, ta bayyana cewa jirgin zai ziyarci Najeriya, Ghana, Senegal, Gambia da Cape Verde.

Read also

Burodi ya zama nama: Tsadar burudo da 'Pure water' ya addabi babban birni Abuja

Tace za ta shiga atisaye na horon manyan kasashen duniya wanda Faransa ke jagoranta wanda zai tattaro abokan hulda na duniya a yankin, wanda aka sani da Exercise Grand African Nemo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce HMS Trent, shi ne jirgin ruwan sojan ruwa na farko da zai fara aiki a yankin na tsawon shekaru uku.

Bayanau sun ce zai gudanar da sintiri na tsaron teku tare da tallafa wa sojojin ruwa ta hanyar taimaka musu wajen habaka manyan dabarun a ruwa da habaka tsare-tsaren ayyukan gaba a yankin.

A cewar sanarwar, tura sojin wata alama ce bayyananniya ta jajircewar Burtaniya na ci gaba da tsunduma cikin yankin, ta inda sama da fam biliyan 6 na kasuwancin Burtaniya ke wucewa a kowace shekara.

Sanarwar ta ambato Ministan Rundunar Sojojin Burtaniya, James Haeppey yana cewa:

"Wannan tayin da aka tura ya nuna Hadin Gwiwar a aikace. Yana nuna yadda da gaske Burtaniya ta Duniya ke tashi tsaye kan matakin duniya don magance kalubalen tsaron kasa da kasa.

Read also

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

"Yin aiki hannu da hannu tare da abokan kawancen mu, muna amfani da Sojojin mu na gaba da aka tura don magance barazanar daga tushe, sanya duniya wuri mafi aminci ga kowa."

Sanarwar ta lura cewa jirgin zai ci gaba da tafiya da rundunar sojan ruwa daga 42 Commando, wanda zai horar da abokan hadin gwiwa a duk yankin a fannin kwarewa daban-daban.

Sanarwar har ila yau ta ambato Mukaddashin Babban Kwamishinan Burtaniya a Najeriya, Ben Llewellyn-Jones, yana cewa:

“Najeriya muhimmiyar abokiyar tsaro ce ga Burtaniya a Yammacin Afirka.
"Kasashenmu biyu suna fuskantar barazanar iri daya kuma muna da burin yin aiki tare da Najeriya don kawar da wadannan kuma don taimakawa inganta tsaron teku a yankin Guinea, gami da fannoni kamar yaki da fashi a teku."

Buhari ya samu lambar yabo daga kasar Ingila ta shugaban da ya gina Najeriya

A baya kunji cewa, an bai wa Shugaban kasa, Muhammadu Buhar lambar yabo ta shugaban da ya gina kasa a wani taron da Jam'iyyar APC, reshen Ingila ta shirya, don murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun 'yancin kai a London.

Read also

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

Sakataren Yada Labarai na kungiyar, Jacob Ogunseye, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka aikewa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi 3 ga watan Oktoba a Abuja, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce an kuma zabi Jagoran Jam’iyyar na Kasa, Bola Tinubu don bashi lambar yabo ta Shugabanci a taron da aka yi ranar 2 ga Oktoba, a Dorchester Hotel da ke Landan a kasar Ingila.

Source: Legit

Online view pixel