Buhari ya samu lambar yabo daga kasar Ingila ta shugaban da ya gina Najeriya

Buhari ya samu lambar yabo daga kasar Ingila ta shugaban da ya gina Najeriya

  • Jam'iyyar APC a kasar Ingila ta karrama shugaba Buhari da lambar yabon shugaba mai gina kasa
  • Hakazalika, Bola Tinubu shi ma an bashi lambar yabon kasancewa shugaba mai tasiri a duk dai a APC ta Ingila
  • Wannan na zuwa ne a cikin bukukuwan cikar Najeriya shekaru 61 da 'yanci a wannan shekarar ta 2021

UK, Landan - An bai wa Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) lambar yabo ta shugaban da ya gina kasa a wani taron da Jam'iyyar APC, reshen Ingila ta shirya, don murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun 'yancin kai a London.

Sakataren Yada Labarai na kungiyar, Jacob Ogunseye, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka aikewa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi 3 ga watan Oktoba a Abuja, Vanguard ta ruwaito.

Read also

Gwamnatin Buhari za ta fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa

Ya ce an kuma zabi Jagoran Jam’iyyar na Kasa, Bola Tinubu don bashi lambar yabo ta Shugabanci a taron da aka yi ranar 2 ga Oktoba, a Dorchester Hotel da ke Landan a kasar Ingila.

Shugaba Buhari da Tinubu sun samu lambobin yabo daga kasar Ingila
Shugaba Buhari da Bola Tinubu | Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

A cewar sanarwar, duk da kalubalen da kasar ke fuskanta a yanzu, makomarta tana da haske mai gamsarwa, ta kara da cewa ya kamata a dauki ranar 'yancin kai a matsayin ranar tunawa kan abubuwan da suka gabata na kasar, yin aiki akan halin da ake ciki da tsara makoma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Punch ta tattaro sanarwar ta nakalto shi yana cewa:

"Lokaci ya yi da za a sake yin aiki, sake-jaddadawa, dubawa da sake fasalin kasar don bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma tsarin aiki don tabbatar da kyakkyawan yanayin rayuwa ga daukacin 'yan kasa."

Jagoran na APC ingila ya lura cewa mai yiwuwa Najeriya ba ta kasance a inda ya kamata ba a matsayin kasa, amma dai a yanzu ta fi da.

Read also

Sanatan APC ya maida wa Sanusi martani kan ikirarin cewa tattalin Najeriya ya kusa ya ruguje

“Mun tsallake halin nadama da hadari da muke ciki kuma yanzu muna samun ci gaba mai yawa tare da sabon tsari a rundunar soji da ta sake samun karfafawa."

Sauya sheka: Gwamna Buni ya karbi mambobin majalisar jihar Anambra 11 zuwa APC

Gwamnan jihar Yobe, kuma shugaban kwamitin tsare-tsaren babban taron jam'iyyar APC na rikon kwarya, Mai Mala Buni ya karbi wasu jiga-jigan siyasar jihar Anambra daga wasu jam'iyyu zuwa APC.

Ana ci gaba da yawaita sauya sheka a cikin wannan shekara, lamarin da ya kawo cece-kuce a jam'iyyun siyasa daban-daban na Najeriya.

cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na gwamna Buni ya fitar a shafinsa na Facebook, mun samu cikakken bayani kan karbar wadannan sabbin shiga ga jam'iyyar APC.

Source: Legit

Online view pixel