Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2022 a ranar Alhamis ga majalisar dokoki

Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2022 a ranar Alhamis ga majalisar dokoki

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatarwa majalisar dokoki daftarin kasafin kudin shekarar 2022
  • Majalisar ce ta sanar da haka yayin zaman ta da ya gudana a yau Talata 5 ga watan Oktoba
  • Shugaban zai gabatar da kasafin kudin ne mai dauke da gyare-gyare a ranar Alhamis 7 ga watan Oktoba

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2022 ga hadin gwiwar majalisar dokokin kasar a ranar Alhamis mai zuwa, Vanguard ta ruwaito.

Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ovie Omo-Agege ne ya bayyana hakan a ranar Talata 5 ga watan Oktoba a zauren majalisar dattawa da ke Abuja.

Ya sanar da hakan ne yayin da yake jagorantar zaman majalisar yayin da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, bai halarci taron ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

Da Duminsa: Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2022 a ranar Alhamis
Shugaba Buhari yayin gabatar da kasafin kudi | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Rahoton Channels Tv ya ce, kafin sanarwar, Sanata Omo-Agege ya sanar da ‘yan majalisar cewa shugaba Buhari ya gabatar da tsarin gyararren kasafin kudi na 2022-2024 na MTEF da Takardar Fiscal Strategy Paper (FSP).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin wasikar da ya aike wa Majalisar Dattawa, Shugaban ya bukaci ‘yan majalisar su amince da takardun tsare-tsare wadanda ya ce za su zama ginshiki da hasashe a cikin kasafin kudin na 2022.

Ya bayyana cewa gyare-gyare sun nuna sabbin sharuddan kasafin kudi a cikin Dokar Masana'antar Man Fetur da aka sanya a kwanan nan, da kuma Dokar Kasafi ta 2022.

Wannan gyaran, a cewar Shugaba Buhari, zai nuna kudaden da za a bai wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) don shirya babban zaben 2023.

Ya yi bayanin cewa gyaran ya kuma tanadi batun alawus na hatsari ga ma’aikatan kiwon lafiya, daidaita albashi ga ma’aikata, da kudade ga yawan jama’a da kidayar gidaje a shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Majalisa ta tabbatar da nadin wanda ya fara karatu tun ba a haife shi ba a cikin mashawartan EFCC

Buhari ya samu lambar yabo daga kasar Ingila ta shugaban da ya gina Najeriya

A wani labarin, an bai wa Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) lambar yabo ta shugaban da ya gina kasa a wani taron da Jam'iyyar APC, reshen Ingila ta shirya, don murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun 'yancin kai a London.

Sakataren Yada Labarai na kungiyar, Jacob Ogunseye, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka aikewa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi 3 ga watan Oktoba a Abuja, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce an kuma zabi Jagoran Jam’iyyar na Kasa, Bola Tinubu don bashi lambar yabo ta Shugabanci a taron da aka yi ranar 2 ga Oktoba, a Dorchester Hotel da ke Landan a kasar Ingila.

A cewar sanarwar, duk da kalubalen da kasar ke fuskanta a yanzu, makomarta tana da haske mai gamsarwa, ta kara da cewa ya kamata a dauki ranar 'yancin kai a matsayin ranar tunawa kan abubuwan da suka gabata na kasar, yin aiki akan halin da ake ciki da tsara makoma.

Kara karanta wannan

Hadimin Jonathan ya bayyana kudirin neman takarar Shugaban kasa, ya shimfida alkawura

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.