Hadimin Jonathan ya bayyana kudirin neman takarar Shugaban kasa, ya shimfida alkawura

Hadimin Jonathan ya bayyana kudirin neman takarar Shugaban kasa, ya shimfida alkawura

  • Dr. Doyin Okupe ya kaddamar da shirin neman tikitin takarar shugaban Najeriya
  • Okupe wanda ya yi aiki da Dr. Jonathan da Obasanjo yace zai iya gyara kasar nan
  • Idan ya dace, Okupe zai inganta rayuwar talaka, kuma ya samar da wutar lantarki

Nigeria - A ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, 2021, tsohon mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya, Doyin Okupe ya bayyana niyyarsa na neman takara.

Jaridar Punch ta rahoto Dr. Doyin Okupe yana cewa zai nemi takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP a zabe mai zuwa na 2023.

Doyin Okupe ya kaddamar da nufinsa a wani jawabi da ya fitar mai taken: ‘2023: Doyin Okupe promises a government that prioritises the needs of the poor as he officially declares presidential ambition.'

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC da ya shiga gidan yari ya fito, yana maganar neman Shugaban kasa

Ofishin yada labaran ‘dan siyasar kudancin Najeriyan ya fitar da wannan jawabi a ranar Talata.

Kamar yadda rahoton da aka fitar ya bayyana, Okupe zai maida hankali ne a kan talakawa idan har ya samu damar zama shugaban kasar Najeriya a zaben 2023.

Hadimin Jonathan
Dr. Doyin Okupe Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Abin da Doyin Okupe ya fada a jawabinsa

“Na yi imani ina da ilmi, da duk abin da ake bukata a siyasa da kwakwalwa da basira wajen shawo kan tabarbarewar sha’anin tattalin arziki, zamantake wa, rashin tsaro, da talaucin da ya yi mana katutu, ya sa ba a jin dadin rayuwa a Najeriya.”
“Ina so in gudanar da gwamnati wanda a karon farko a tarihi za ta maida hankali wajen kula da dukiya da halin da rayuwar da musamman talaka yake ciki." - Dr. Okupe.

Kara karanta wannan

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

Dr. Okupe ya yi alkawari cewa idan aka ba shi ragamar kasar nan, zai kawo gyara a yadda ake tsara kasafin kudi ta yadda talaka ne zai amfana da dukiyar kasa.

Kamar yadda Leadership ta fitar da rahoto, Okupe ya sha alwashin cewa idan har ya samu mulki, 30% na kasafin kudi tun daga 2023 zai tafi wajen jin dadin al’umma.

Baya ga haka, ‘dan siyasar yace zai kara adadin karfin wutan lantarkin da Najeriya take da shi zuwa megawatt 30, 000, yace zai yi wannan ne a cikin shekaru uku.

Sarakunan Legas sun ce sai Tinubu

A jiya aka ji Sarakuna akalla 65 da ke Legas sun bayyana cewa suna so tsohon Gwamna kuma jigo a jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya nemi kujerar Shugaban kasa.

Duk da 'dan siyasar yana kasar waje, Sarakunan sun nuna goyon bayansu ga takarar Bola Tinubu a lokacin da suka yi wani taro da kungiyar SWAGA 2023 a Ikeja jiya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

Asali: Legit.ng

Online view pixel