Majalisa ta tabbatar da nadin wanda ya fara karatu tun ba a haife shi ba a cikin mashawartan EFCC

Majalisa ta tabbatar da nadin wanda ya fara karatu tun ba a haife shi ba a cikin mashawartan EFCC

  • Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin mutum 5 da shugaba Buhari ya mika mata sunansu domin zama mashawartan EFCC
  • Sai dai, daga cikinsu akwai Muhammad Yahaya wanda takardunsa suka bayyana ya fara firamare shekara 1 kafin a haifesa
  • Har ila yau, takardun Yahaya sun nuna cewa a yayin da yake kwalejin horar da malamai, ya na kwalejin koyar da ayyukan gudanarwa

FCT, Abuja - A ranar Talata, majalisar dattawan Najeriya ta amince da nadin Yahaya Muhammad, a matsayin daya daga cikin mashawartan hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, wanda takardun sa suka nuna ya fara makarantar firamare da shekara daya kafin a haife shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Muhammad ya na daya daga cikin mutum biyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zaba kuma majalisar ta aminta da su a ranar Talata.

Read also

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

Majalisa ta tabbatar da nadin wanda ya fara karatu tun ba a haife shi ba a cikin mashawartan EFCC
Majalisa ta tabbatar da nadin wanda ya fara karatu tun ba a haife shi ba a cikin mashawartan EFCC. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

Tabbatarwa tare da amincewa da wadanda Buhari ya zaba ya biyo bayan rahoton da kwamitin yaki da rashawa na majalisar, wanda Sanata Suleiman Abdu Kwari ke shugabanta ya mika.

A wata wasika mai kwanan wata 17 ga Satumba, Buhari ya bukaci dattawan da su tabbatar da nadin sakatare tare da mambobin majalisar mashawartan EFCC.

Wadanda aka tabbatar tare da Muhammad sun hada da George Abang Ekungu, Secretary (Cross River); Luqman Muhammed (Edo); Anumba Adaeze (Enugu) da Kola Raheem Adesina (Kwara).

A gabatarwarsa, Sanata Kwari ya ce kwamitin ya duba takardun wadanda aka zaba kuma sun cika duk abinda ake bukatar na gogewa da nagarta wurin yin aikin da aka zabe su domin shi.

Ya ce babu wani rahoton tsaro ko kuma korafi na game da su, don haka ya bukaci majalisar da ta tabbatar da su, Daily Trust ta wallafa.

Read also

An tsaurara tsaro yayinda Shugaba Buhari ke shirin gabatar da kasafin kudin 2022 yau

Sai dai, Sanata Hassan Hadejia ya yi kira ga abokan aikinsa kan banbancin da ke cikin takardun Muhammad inda suke nuna an haife shi a ranar 29 ga watan Samtumban 1969 kuma ya fara makarantar firamare a shekarar 1968.

Ya ce: "Bari in janyo hankalin 'yan majalisar kan banbancin da ke rubuce a takardun Alhaji Yahaya Muhammad a shafi na takwas inda ya fara firamare kafin a haifesa.
"Hakazalika, a bangaren shekarar da yayi karatu, ya halarci makarantar horar da malamai da ke Borno daga 1975 zuwa 1988 kuma ya halarci kwalejin gudanarwa tsakanin 1980 zuwa 1981. Idan akwai kuskure wurin rubutu, ina ganin ya dace a gyara."

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege wanda ya shugabanci zaman, ya yi biris da wannan korafin inda ya tabbatar da nadin.

Duk da tsoma bakin Diflomasiyya: 'Yan Ghana sun cigaba da muzguna wa 'yan kasuwan Najeriya

A wani labari na daban, watanni goma bayan jerin sasanci da aka yi tsakanin gwamnatin Najeriya da hukumomin Ghana wanda aka yi shi domin shawo kan matsalar rikicin da ya kawo rufe shagunan 'yan kasuwan Najeriya a Ghana, lamarin ya sake barkewa, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Read also

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

'Yan Najeriya masu tarin yawa sun rasa hanyar neman abincinsu saboda rikicin da ya sake barkewa duk da kiran gwamnatin tarayya da aka yi domin ta kai musu dauki.

Daily Trust ta tattaro cewa, tsakanin ranakun ashirin zuwa da hudu na watan Satumba, 'yan kungiyar 'yan kasuwan Ghana, sun rufe wasu shagunan 'yan Najeriya a cikin zanga-zangarsu ta dakile bakin haure daga kasuwanci a kasar.

Source: Legit

Online view pixel