Yanzu-Yanzu: An yi wa jami'in DSS kisar gilla a jihar Imo

Yanzu-Yanzu: An yi wa jami'in DSS kisar gilla a jihar Imo

  • An halaka wani jami'in hukumar DSS a Owerri babban birnin jihar Imo
  • Mr Deacon Daniel Opara, dan uwan marigayin ya tabbatar da rasuwarsa
  • Amma 'yan uwansa na zargin lauje cikin nadi duba da cewa an masa karin girma a baya-bayan nan

Imo - An yi wa jami'in hukumar yan sandan farin kaya DSS, kisar gilla a garin Owerri, babban birnin jihar Imo, Daily Trust ta ruwaito.

Hakan na faruwa ne kasa da awa 48 bayan kona ofishin hukumar da aka yi a Nnewi, jihar Anambra.

Yanzu-Yanzu: An yi wa jami'in DSS kisar gilla a jihar Imo
Yanzu-Yanzu: An yi wa jami'in DSS kisar gilla a jihar Imo
Asali: Original

Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa an bindige jami'in mai suna Prince Nwachinaemere Ezemuonye Ozuzu, daga Umuoyo, Irete, karamar hukumar Owerri West a hanyar Owerri/Onitsha.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

An ce an tura jami'in ya yi wani aiki ne a Anambra awanni kadan bayan kona ofishin DSS na Nnewi.

An kashe shi ne a lokacin da ya ke hanyarsa ta komawa wurin aikinsa.

A halin yanzu babu cikakken bayanin kan yadda ya mutu duba da cewa wani rahoton ya ce ya mutu ne sakamakon kuskuren harbi.

An ce wani abokin aikinsa ne ya harba bindiga bisa kuskure kuma harsashin ya same shi.

Daya daga cikin yan uwansa, Deacon Daniel Opara, wanda ya tabbatar da rasuwarsa ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki.

Ya ce:

"Ba mu samu cikaken bayani kan ainihin abin da ya faru ba domin an yi ikirarin cewa wani dan sanda da suke aikin hadin gwiwa tare ne ya bindige shi bisa kuskure a wurin aiki a jihar Anambra.
"Iyalansa na zargin akwai lauje cikin nadi duba da cewa a baya-bayan nan aka yi masa karin girma.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: IGP ya tura sabon kwamishina da dakaru na musamman

"Ya fara aiki da DSS kimanin shekaru hudu zuwa biyar da suka gabata kuma yana da aure da 'ya'ya hudu."

Ba a samu ji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, CSP Mike Abattam ba domin wayansa ya yi ta ringing amma bai daga ba.

Mutane su na barazanar halaka ni, Likitan Najeriya da ya buɗe wurin gwajin DNA tare da yin rahusa na kashi 70

A wani labarin daban, wani likita wanda ya bude wurin gwajin kwayoyin halitta na DNA a anguwarsu ya bayyana yadda wasu mutane suke barazanar halaka shi a shafin sa na dandalin sada zumunta sakamakon zargin zai zama kalubale ga aurensu.

Kamar yadda Pulse Nigeria ta ruwaito, likitan mai suna Dr Penking ya bayyana cewa zai bude wurin gwajin DNA din a jihar Legas ne kuma zai samar da rahusar kaso 75 bisa dari a watan Oktoba.

Mutane da dama sun yarda da cewa wannan rahusar za ta bai wa maza da yawa damar tabbatar wa idan su ne iyayen yaran su na hakika, hakan ya kada ruwan cikin jama’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel